Da duminsa: Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a

Da duminsa: Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a

- Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a

- Mataimaki na musamman ga Buhari a fannin yada labarai, Femi Adesina yace za a fara da karfe 8:30 na yammacin Juma'a

- Kamar yadda ya bayyana a wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, tattaunawar za ta kasance mai ilmantarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin ranar Juma'a.

Femi Adesina, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasan a fannin yada labarai, ya bayyana hakan a ranar Juma'a a wata takarda da ya fitar.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince zai yi tattaunawa ta musamman da NTA daga karfe 8:30 na yammacin ranar Juma'a, 11 ga watan Yunin 2021.

KU KARANTA: Sunayen biranen duniya mafi muni da za a iya rayuwa a 2021, Legas ce ta biyu

Da duminsa: Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a
Da duminsa: Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a
Asali: Original

“An yi alkawarin tattaunawar zata zamo mai ilimantarwa. A kiyaye lokaci," takardar da ya wallafa a Facebook tace.

A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da Arise TV inda ya taba manyan al'amuran da suke cin tuwo a kwarya a kasar nan.

A wani labari na daban, fitacce kuma jarumin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari ya bayyana yadda ya samu barazana sama da 100 daga Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami.

A wata takardar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni kuma legit.ng ta gani, babban dan sandan yace babu wata barazana da za ta hana shi da rundunar shi baiwa 'yan Najeriya kariya.

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaron kasar nan ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin yaki da ta'addanci. Ya tabbatar da cewa dukkan 'yan ta'adda da makasa dake fadin kasar nan sai sun ji kunya da izinin Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng