A lokacin da aka kwatanta mu da birai, Twitter ta ki goge wallafar, Lai Mohammed

A lokacin da aka kwatanta mu da birai, Twitter ta ki goge wallafar, Lai Mohammed

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ce katsalandan da Twitter tayi wa Najeriya yasa aka dakatar da ita

- Ya bada labarin yadda Twitter ta bar Nnamdi Kanu da sauran masu tada kayar baya a kasar nan suna cin karensu babu babbaka

- Mohammed yace akwai lokacin da suka dinga rokon Twitter ta goge wallafar da aka kwatanta 'yan Najeriya da birai amma ta ki

Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya kare gwamnatin tarayya kan yadda ta dakatar da al'amuran Twitter a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Yau mako daya cif kenan da Mohammed ya sanar da hukuncin da gwamnatin tarayya ta yankewa Twitter bayan an zargesu da katsalandan a al'amuran kasar nan.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas

A lokacin da aka kwatanta mu da birai, Twitter ta ki goge wallafar, Lai Mohammed
A lokacin da aka kwatanta mu da birai, Twitter ta ki goge wallafar, Lai Mohammed yace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsawon shekaru 6, mata da 'ya'yanta na kwana a bandaki bayan mijinta ya tsere

Tun bayan nan, jama'a sun matsantawa gwamnatin tarayya domin ta dage dokar haramta Twitter.

A yayin jawabi a wani shiri a NTA na ranar Juma'a, Mohammed ya zargi Twitter da barin Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da cin karensu babu babbaka, Daily Trust ta ruwaito.

"Kafin dakatar da Twitter, mun dinga rokonsu da su cire wallafar da aka kwatanta Najeriya da gidan zoo tare da kwatanta mu da birai.

"Mun rokesu da su goge wallafa da aka ce idan sojan Najeriya ya shiga Biafra, toh mutuwarsa ta zo.

"Amma sai Twitter tace wadannan wallafar basu take dokokinsu ba. Abu har ya kai ana kaiwa 'yan sanda da sojoji hari, hakan yasa muka ce ba zamu hakura ba, dole ne mu dakatar da ayyukanta," yace.

A wani labari na daban, kwamitin majalisar wakilai a kan matasa ya ce babu wani shiri na haramta hidimar kasa (NYSC) a yanzu.

Shugaban kwamitin, Yemi Adaramodu, ya sanar da hakan a Abuja a ranar Alhamis a taron kaddamar da littafai tara na NYSC da kuma fim na farko domin tunawa da kafa hukumar a shekaru 48 da ta gabata.

Kamar yadda yace, NYSC tana daga cikin shirin kasa masu nasara wanda ya tabbatar da hadin kai a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel