'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari

'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace mulkinsa ya yi matukar kokari idan aka duba da yadda ya zo ya karba kasar

- A cewar Buhari, 'yan Najeriya su dinga musu adalci idan suka tashi yanke hukunci kan mulkinsa tun daga 2015

- Buhari wanda ya tattauna da gidan talabijin na kasa (NTA), ya ce babu shakka sun kokarta ballantana a fannin arewa maso gabas da kudu kudu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa yayi kokari tun bayan da suka hau karagar a 2015.

Buhari ya sanar da hakan ne a tattaunawa ta musamman da yayi da gidan talabijin na kasa (NTA) a ranar Juma'a.

Shugaban kasan ya bukaci 'yan Najeriya da su dinga yi wa mulkinsa adalci idan suka tashi yanke hukunci. Ya kara da cewa jama'a su dinga duba abinda ya samar a mulkinsa da kuma abinda akwai kafin ya hau karagar jagorancin Najeriya.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas

'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari
'Yan Najeriya su dinga mana adalci, mulkinmu yayi matukar kokari, Buhari. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Daga bisani, majalisa ta tsahirta, ta hakura da yunkurin haramta hidimar kasa

"Ina son 'yan Najeriya su dinga yi wa mulkin nan adalci. Sun kasance masu tuna baya lokacin da ba mu iso ba, ballantana a abubuwan da suka shafi arewa maso gabas da kudu kudu na kasar nan," yace.

"Zan so 'yan Najeriya su dinga tuna wadannan abubuwan lokaci zuwa lokaci kuma ina da tabbacin bamu yi mugun abu ba."

A wani labari na daban, hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna ta rufe dukkan makarantar har sai baba ta gani. Ta umarci dukkan dalibai da su gaggauta barin makarantar.

Wannan ya biyo bayan harin da miyagun 'yan bindiga suka kai makarantar kuma suka sace dalibai takwas daga dakunan baccinsu tare da malami biyu daga kwatas din malaman.

A wata takardar da mukaddashin rijistra na makarantar, Mahmoud Kwarbai ya fitar a ranar Juma'a, ya ce hukumar tace wannan matakin an dauke shi ne sakamakon tashin hankalin da harin ya janyo tsakanin daliban.

Amma kuma wannan umarnin bai shafi daliban da zasu fara rubuta jarabawar IJMB ba a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a ranar Talata, 15 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel