Daga bisani, majalisa ta tsahirta, ta hakura da yunkurin haramta hidimar kasa
- Majalisar tarayya ta rissina inda tace ta hakura a cigaba da hidimar kasa a Najeriya
- Shugaban kwamitin matasa, Yemi Adaramodu ya ce majalisar tace babu bukatar soke NYSC
- Kamar yadda suka tabbatar, NYSC ta habaka hadin kai ga kabilu da sassan kasar nan
Kwamitin majalisar wakilai a kan matasa ya ce babu wani shiri na haramta hidimar kasa (NYSC) a yanzu.
Shugaban kwamitin, Yemi Adaramodu, ya sanar da hakan a Abuja a ranar Alhamis a taron kaddamar da littafai tara na NYSC da kuma fim na farko domin tunawa da kafa hukumar a shekaru 48 da ta gabata.
Kamar yadda yace, NYSC tana daga cikin shirin kasa masu nasara wanda ya tabbatar da hadin kai a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: APC ce za ta fitar da wanda ya gaje ni, ba ni ba, Shugaba Buhari
KU KARANTA: Bidiyon mutumin da yake wasa da zakuna 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1
A wata bukata da Awaji -Inombek Abiante, ya mika gaban majalisar har an karanta karo na biyu domin aminta da daina hidimar kasa, Daily Nigerian ta ruwaito.
Amma a jiya Adaramodu ya ce: "Kowa na da ikon mika bukata, amma kakakin majalisa da sauran 'yan majalisa suna son al'amarin ya cigaba a Najeriya.
"Babu inda hukumar za ta je kuma bashi daga cikin shirin majalisar dattawa na dakatar da shi. Ina son ku san muna tare da ku, dari bisa dari muna tare."
Gwamnan jihar Nasarawa, Abduallhi Sule ya ce babu dalilin soke NYSC, inda ya jaddada cewa babu abinda ya kai tsaro, "babu abinda ya kai hadin kai kuma NYSC ce ma'anar hadin kai a Najeriya."
A wani labari na daban, Fitacce kuma jarumin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari ya bayyana yadda ya samu barazana sama da 100 daga Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami.
A wata takardar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni kuma legit.ng ta gani, babban dan sandan yace babu wata barazana da za ta hana shi da rundunar shi baiwa 'yan Najeriya kariya.
Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaron kasar nan ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin yaki da ta'addanci. Ya tabbatar da cewa dukkan 'yan ta'adda da makasa dake fadin kasar nan sai sun ji kunya da izinin Ubangiji.
Asali: Legit.ng