Da duminsa: Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas

Da duminsa: Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas

- Shugaba Muhammadu Buhari ya koma garin Abuja bayan kai ziyarar aiki ta kwana daya garin Legas

- A ziyarar da shugaban kasan ya kai, ya kaddamar da dogo mai tsayin kilomita 157 daga Legas zuwa jihar Ibadan

- Shugaban kasan ya tabbatar da cewa mulkinsa zai cigaba da baiwa sufuri irin na jiragen kasa fifiko

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar aikin kwana daya da ya kai cibiyar kasuwanci ta Najeriya, Legas.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma garin Abuja bayan ziyarar aikin kwana daya da ya kai jihar Legas," hadiminsa na musamman a harkar yada labarai, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shugaban kasar Najeriyan mai shekaru 78 ya ziyarci jihar Legas ne domin kaddamar da wasu ayyuka da suka hada da titin jirgin kasa mai nisan kilomita 157 a filin jirgin kasa na Mobolaji dake Ebutte Metta.

KU KARANTA: Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice

Da duminsa: Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas
Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar kwana 1 da ya kai Legas. Hoto daga ChannelsTV
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon mutumin da yake wasa da zakuna 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1

A yayin bikin kaddamar da dogon a filin jirgin kasa na Mobolaji, Buhari ya jaddada cewa mulkinsa zai cigaba da baiwa tsarin jiragen kasa fifiko, Channels TV ta ruwaito.

Ya kwatanta aikin da wani babban cigaba da nasara da mulkinsa na samar da fannin sufuri ga fasinjoji da kuma daukar kaya.

"Shugaban kasa ya sha alwashin cewa mulkinsa zai cigaba da baiwa tsarin jiragen kasa fifiko a fannin sufuri domin hakan zai kawo sauyi a fannin ma'aikatu a kasar nan," takardar da mai baiwa Buhari shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina ta tabbatar.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam'iyyar APC mai mulki ce zata yanke hukuncin wanda wanda zai gaje shi ba wai shi da kansa ba.

Ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Arise Tv yayin wata tattaunawa ta musamman, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kasan ya ce, "A kan wanda ya gajeni, abinda wannan mulkin zai iya shine ya tabbatar da karkon APC har bayan saukarmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel