Da duminsa: Ban gamsu da tattalin arzikin kasar nan ba, Buhari

Da duminsa: Ban gamsu da tattalin arzikin kasar nan ba, Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa bai gamsu da yanayin tattalin arzikin Najeriya ba

- A cewarsa yayin hira da aka yi dashi a NTA, hakan ce ta sa yake ta kokarin kawatarwa masu saka hannayen jari kasar nan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace saka hannayen jari daga kasashen ketare zai bada gudumawa wurin samar da aikin yi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai gamsu da yadda tattalin arzikin kasar nan yake tafiya ba.

Buhari, wanda ya sanar da hakan a tattaunawa ta musamman da yayi da NTA, ya kara da cewa mulkinsa na aiki tukuru wurin ganin ta janyo masu zuba hannayen jari kai tsaye a Najeriya.

"Ban gamsu da yanayin tattalin arziki ba. Hakan ne yasa nake ta janyo kasashen ketare domin basu damar amincewa tare da zuba hannayen jari a Najeriya. Hakan ne zai samar da aikin yi," yace.

Najeriya ta fita daga mugun yanayi na karayar tattalin arziki wanda ta kwashi shekaru 33 bata shiga kamarsa ba.

KU KARANTA: Boko Haram da 'yan bindiga sun yi min barazana sama da sau 100, DCP Abba Kyari

Da duminsa: Ban gamsu da tattalin arzikin kasar nan ba, Buhari
Da duminsa: Ban gamsu da tattalin arzikin kasar nan ba, Buhari
Asali: Original

KU KARANTA: Daga bisani, majalisa ta tsahirta, ta hakura da yunkurin haramta hidimar kasa

Kasar nan ta fuskanci hauhawar rashin aikin yi da aka dade ba a ga irinsa ba a 2020 inda kusan kashi 40 na 'yan kasar ke rayuwa cikin mugun kangin talauci.

Amma kuma tattalin arzikin kasar ya ki daidaituwa saboda muguwar illar da annobar korona tayi wa duniya.

A wani labari na daban, hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna ta rufe dukkan makarantar har sai baba ta gani.

Ta umarci dukkan dalibai da su gaggauta barin makarantar. Wannan ya biyo bayan harin da miyagun 'yan bindiga suka kai makarantar kuma suka sace dalibai takwas daga dakunan baccinsu tare da malami biyu daga kwatas din malaman.

A wata takardar da mukaddashin rijistra na makarantar, Mahmoud Kwarbai ya fitar a ranar Juma'a, ya ce hukumar tace wannan matakin an dauke shi ne sakamakon tashin hankalin da harin ya janyo tsakanin daliban.

Amma kuma wannan umarnin bai shafi daliban da zasu fara rubuta jarabawar IJMB ba a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a ranar Talata, 15 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng