Twitter ya yi magana kan batun zaman sulhu da gwamnatin Nigeria

Twitter ya yi magana kan batun zaman sulhu da gwamnatin Nigeria

  • Kamfanin Twitter ya tabbatar da cewa a shirye ya ke ya zauna da gwamnatin Nigeria domin tattauna kan yadda za a dage dakatarwar da aka yi masa
  • A ranar Laraba ne Ministan Labarai da Al'adu na Nigeria ya sanar da cewa kamfanin ya tuntube su yana neman a zauna a teburin sulhu ka dakatarwar
  • Tunda farko da gwamnatin Nigeria ta dakatar da kamfanin ne kan zargin ana amfani da shi wurin wargaza kan al'ummar kasa da taimakawa miyagu

Babban kamfanin dandalin sada zumunta na Twitter ya ce ya sanar da gwamnatin Nigeria cewa a shirye yake ya zauna da ita domin a tattauna kan dakatar da ayyukansa da aka yi a kasar, The Punch ta ruwaito.

Ministan Labarai da Al'adun Nigeria, Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed, Ministan Al'adu da Labarai na Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

A ranar Juma'a da ta gabata ne gwamnatin tarayyar Nigeria ta dakatar da ayyukan kamfanin na Twitter a kan zarginsa da 'raba kan al'umma da taimakawa wajen aikata miyagun ayyuka.'

A ranar Laraba, Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya sanar da dakatarwar ya shaidawa manema labarai cewa mahukunta a kamfanin na Twitter suna neman 'a zauna a tattauna' domin warware matsalar da ta janyo aka dakatar da kamfanin.

A bangarensa, kamfanin na Twitter ya tabbatar da kalaman na Minista Lai Mohammed a ranar Juma'a 11 ga watan Yuni kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

"A yau mako guda kenan da aka dakatar da Twitter a Nigeria. Mun sanar da gwamnatin Nigeria cewa a shirye muke mu zauna da su a teburun sulhu domin tattaunawa kan yadda za a dawo da ayyukan kamfanin. Muna goyon bayan bawa kowa yancin bayyana ra'ayinsa #OpenInternet everywhere. #KeepitOn.”

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164