Da Duminsa: NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi ranar June 12, ta bayyana dalili
- Kungiyar daliban Nigeria na kasa, NANS, ta sanar da dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a ranar June 12 kan sace dalibai
- Sunday Asefon, shugaban kungiyar na kasa ya ce an dakatar da zanga-zangar ne domin akwai yiwuwar masu manufofin siyasa za su shiga su lalata lamarin
- Shugaban na NANS ya ce dakatarwa suka yi domin kare rayyukan dalibai amma nan gaba za su sanar da sabon ranar yin zanga-zangan
Kungiyar daliban Nigeria na kasa, NANS, ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a ranar 12 ga watan Yuni 'June 12' a fadin kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon ne ya bayyanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Juma'a.
The Punch ta ruwaito cewar shugaban na NANS ya ce an shirya yin zanga-zangan ne domin nuna damuwa kan rashin tsaro a kasar musamman yawan sace dalibai da ake yi.
DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi
Dalilin Janye Zanga-Zangar
Sai dai, Asefon ya ce wasu yan siyasa da ke da wata maufarsu na daban sun shirya tsaf domin kutsawa cikin zanga-zangar da nufin 'cimma wasu manufofinsu na siyasa da son zuciya.'
Ya kuma ce kungiyar daliban bata da wata alaka da 'yan aware ko yan siyasa da masu rajjin kare hakkin bil adama da ke jagorancin tafiyar ganin sai Buhari ya sauka daga mulki wato 'Buhari-must-go' da suka shirya yin zanga-zanga a ranar Asabar.
Ya ce, "Bisa la'akari da halin tsaro da ake ciki a yanzu da hadarin da mambobin mu ka iya shiga idan wasu sunyi kutse sun sauya wa zanga-zangar alkibila, ni da sauran shugabannin NANS, muna sanar da dakatar da zanga-zangar da muka shirya yi a ranar June 12.
KU KARANTA: Buhari: Na Bada Umurnin Ɗaukan Sabbin Ƴan Sanda 10,000 da Yi Musu Ƙarin Albashi
"Mun dakatar ne domin kada a samu matsala tsakanin mu da jami'an tsaro da a yanzu suke cikin shirin ko ta kwana domin kare kayayyakin kasa da tabbatar da doka da oda sakamakon wasu zanga-zangar da aka shirya yi a ranar.
"Mun yi niyyar yin zanga-zanga ne domin neman inganta tsaro da walwalar dalibanmu don haka ba zamu saka rayuwarsu cikin hadari ba wurin bayyana damuwarmu."
Asefon ya fayyace cewa ba soke zanga-zangar aka yi ba, dakatarwa aka yi kuma nan gaba za a sanar da sabon ranar da za a yi.
A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.
Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.
Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng