Bidiyon mutumin da yake wasa da zakuna 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1

Bidiyon mutumin da yake wasa da zakuna 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1

- Wani masoyin zakuna yayi abinda jama'a da yawa ba zasu iya ba domin gani zasu yi tamkar siyar da rai ne

- Balaraben mutumin an gan shi a wani bidiyo yana wasa da zakunan biyu a kan gadonsa ba tare da nuna tsoro ba

- Mutumin saboda tsabar karfin hali har saka hannunsa yayi cikin bakin zaki daya, lamarin da ya janyo cece-kuce

Wani mutum ya bayyana cewa hatta namun daji za a iya ajiyesu a cikin gida. Balaraben ya ajiye zakuna biyu a matsayin abokan rayuwarsa kuma ya bayyana su a kafar sada zumunta.

A wani bidiyo da aka wallafa a Instagram, shafi mai suna @kingtundeednut, jama'a sun sha mamaki. Mutumin yana ta wasa da zakunan a kan gadonsa.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom

Bidiyon mutumin da yake wasa da zakanya 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1
Bidiyon mutumin da yake wasa da zakanya 2 a kan gadonsa har yana saka hannu a bakin 1. Hoto daga @kingtundeednut
Asali: Instagram

KU KARANTA: Mutumin da ya kwashe shekaru 50 yana tara motoci kasaitattu ya tara har 3000

A bidiyon dake ta yawo a kafar sada zumunta, duk wanda ya kalla ya tsorata da yadda balaraben bai nuna ko dar ba yayin da yake wasa da zakuna a kan gadonsa.

A wurin da yafi baiwa jama'a masu kallo mamaki, shine inda ya sumbaci kan daya daga cikin zakunan kuma ya saka hannunsa a bakinta kamar yana nuna mata ko zata ciza.

Kamar yadda aka san 'yan Najeriya, ba zasu taba shiru ba bayan ganin bidiyon, ga abinda wasu daga ciki ke cewa:

@scoobynero cewa yayi: "Ai ni ko mutumin ba zan yadda in taba shi ba!!! Kada ya zamto tamkar sun shafa mishi wasu daga cikin halayyarsu."

@toysley tace: "A yanzu dai duk wasa da dariya ne, har sai lokacin da zakunan suka kai masa cizo."

@callme_frost tsokaci tayi da cewa: "Amma 'yan Najeriya ba zasu iya wannan ba koda kuwa suna da kudi."

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce kamfanin Twitter, ya garzaya domin neman sasanci da gwamnatin Najeriya.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya.

Ya bayyana cewa tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu saboda an samu rahotanni na gagarumar asarar da twitter ta dinga tafkawa na biliyoyi, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng