Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice

Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice

- Babban dan wasan damben nan na kasar Amurka, Floyd Mayweather ya bayyana agogon hannun da ya siya $18,000,000

- Matashin mai shekaru 44 a duniya wanda aka fi sani da 'money man' ya bayyana kudin agogon ne yayin da ya halarci wani shiri

- Mayweather ba a agogo ya tsaya ba, ya mallaki kasaitattun motoci a garejinsa duk ta hanyar sana'arsa da yake

Fitaccen dan wasan damben nan Floyd Mayweather ya bayyana hadadden agogon hannunsa mai darajar $18,000,000 wanda ya kai N8.9 biliyan yayin da ya halarci wani shirin gidan talabijin.

Babu shakka idan aka ce Floyd Mayweather na daga cikin masu kudi a bangaren masu wasanni a duniya ganin yadda ya azurce.

Kamar yadda bidiyon da ya wallafa a Instagram ya nuna, Floyd Mayweather ya bayyana cike da farin ciki yayin da yake hira da wanda suke shirin tare. Daya daga cikinsu ya hango agogon dake hannun Floyd inda ya tambayesa nawa ya siya kuma ya sanar da shi.

Dukkansu sun gigice bayan sun ji kudin da Floyd Mayweather ya siya agogon ya kai $18,000,000. Sun kara da bukatar mai daukan hoton da ya kara haskawa masu kallo agogon yayin da Floyd Mayweather ke ta murmushi.

KU KARANTA: Gwamnati ta fadi warwas a wurin baiwa 'yan Najeriya kariya, Dan majalisar APC

Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice
Arziki: Floyd May-weather ya bayyana da agogon N8.9 biliyan, jama'a sun gigice. Hoto daga Louis Grasse
Asali: Getty Images

Baya ga kudaden da Floyd ke kashewa a kayan karau, yana matukar kaunar motocin alfarma domin kuwa ya mallaki kala-kala a garejinsa a Amurka.

Yana siyan motocin zamani, na gani, na fadi tare da bugawa a jaridu. In dai arziki ake magana da dukiya, toh tabbas ya tara su.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter salo ne na kawar da hankalin 'yan kasa daga gazawar FG, Ortom

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce kamfanin Twitter, ya garzaya domin neman sasanci da gwamnatin Najeriya.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya.

Ya bayyana cewa tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu saboda an samu rahotanni na gagarumar asarar da twitter ta dinga tafkawa na biliyoyi, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel