Sabon Shugaban Hafsun Soja ya fara taba manyan Sojoji, ya canzawa wasu Jami'ai wurin aiki

Sabon Shugaban Hafsun Soja ya fara taba manyan Sojoji, ya canzawa wasu Jami'ai wurin aiki

  • Laftanan Janar Faruk Yahaya ya fitar da sababbin nadin mukamai a gidan soja
  • Shugaban sojojin kasan ya nada sabon shugaban dakarun Operation Hadin kai
  • Birgediya Janar A. M Umar shi ne shugaban sojojin da ke ofishin Hafsun Sojoji

Kwanaki kadan da shigansa ofis, Laftanan Janar Faruk Yahaya ya fara da yin wasu sauya-sauye, inda ya canzawa wasu jami’an sojojin kasa wurin aiki.

Jaridar The Nation ta ce kakakin gidan sojan kasa Birgediya Janar Mohammed Yerima ne ya bada sanarwar wannan sauyi da aka samu a ranar Alhamis.

Daga cikin canza-canzen da aka yi, Manjo-Janar C.G. Musa ne ya zama sabon shugaban rundunar Operation Hadin Kai, shi ne zai cike gurbin da Hafsun ya bari.

KU KARANTA: Najeriya za ta rasa manyan Sojoji bayan nadin sabon COAS

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Shi kuma Birgediya Janar A. M Umar ya zama shugaban duka ma’aikatan ofishin hafsun sojojin kasa. Janar AM Umar zai bar makarantar koyon yaki na Najeriya.

Sauran wadanda sauyin ya shafa sun hada da: Birgediya Janar AE Abubakar daga sashen horaswa da gudanarwa, ya zama shugaban birged na hedikwata ta 22.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Birgediya Janar KO Ukandu ya bar ofishin hafsun sojojin kasa, ya zama darektan makarantar tsaro.

Sanarwar ta ce Birgediya Janar NU Muktar zai tashi daga ofishin jakadancin Najeriya da ke Isalamabad, zai zama darektan harkar shigo da kaya a gidan soja.

Laftanan Janar Faruk Yahaya
Shugaban Hafsun Sojojin kasa Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Buratai ya yi wasu sababbin nade-naden mukami a gidan Soja

Shi kuma Birgediya Janar IB Abubakar ya bar wata makarantar horas da sojojin yaki, ya koma hedikwata a matsayin mataimakin darekta wajen gudanarwa.

Manjo Janar FO Omoigui ya bar Operation Hadin Kai, ya koma wata cibiya. Kanal KE Inyang, Kanal OO Braimah da Kanal IP Omoke suna cikin wadanda aka taba.

Kara karanta wannan

Yadda Kwanturolan Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano

Jaridar Vanguard ta ce haka zalika an dauke Birgediya Janar AJS Gulani, ya zama shugaban birged na 24 a hedikwata. An yi kira gare su, su yi aiki bakin kokarinsu.

The Guardian ta ce an saba ganin irin wannan da zarar an samu sabon shugaban hafsun sojoji. An yi haka a lokacin da Marigayi Janar A. Ibrahim ya shiga ofis.

Shi kansa Janar Mohammed Yerima ya na shirin sauka daga mukaminsa na mai magana da yawun bakin sojojin Najeriya, zai ba Onyema Nwachukwu wuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel