Ba da dadewa ba: An yi wasu sababbin nadin mukami a gidan Soja
Mun samu labari jiya daga hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN cewa an yi wasu sababbin sauye-sauye a gidan sojan Najeriya. Wannan canjin aiki da aka yi ya shafi manyan jami’an sojojin ne.
A.A.Tarfa, wanda shi ne mai kula da rundunar kasar da ke koyon harbi ya bar matsayin sa inda aka maida sa zuwa babbar cibiyar nan ta Martin Luther Agwai mai kwantar da fitina da kuma lura da sha’anin kawo zaman lafiya a Duniya.
A jiya ne Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka wanda shi ne Darektan yada labarai na sojojin Najeriya ya bayyana cewa an kuma canza Manjo Janar M. Mohammed daga matsayin babban kwamanda watau GOC na Runduna ta I.
Haka kuma an cire Manjo Janar C.T. Olukoju wanda kafin yanzu yake lura da Signal Corps daga wajen, an maida sa Hedikwata zuwa wata sabuwar cibiya da aka kafa mai suna Nigerian Army Simulation Centre (NASIMC) inda ya zama Darekta.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa wasu Bayin Allah wuta ana zaune kalau
Wannan sauye-sauye da aka yi ya taba Manjo Janar C.U. Agulanna wanda ke cibiyar bincike na sojojin kasar watau NARC, da kuma Manji Janar F. Yahaya wanda shi ne Sakataren gidan Sojan Najeriya da kuma Manjo Janar AR Bakare.
Sababbin nadin da aka yi sun hada da Birgediya Janar, da S.T. Shafaru. Sauran wadanda aka ba sabon matsayi a kasar sun hada da B.Y. Baffa, U.B. Abubakar, E.E. Emekah, da kuma wani babban Kanal mai suna E.C. Obi-Osang a karshe.
Darektan yada labaran yace an kuma canzawa Manjo Janar U.S. Yakubu wajen aiki zuwa sashen koyon harbi yana mai maye gurbin Janar A.A Tarfa. Har wa yau an taba wasu manyan Sojoji wanda su ke kan mataki na Birgediya Janar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng