Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti

Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti

- Shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya, reshen Makurdi yana kwance a gadon asibiti bayan ya sha lugude hannun jami'an EFCC

- Kamar yadda Barista Justin Gbagir ya sanar, ya je ofishin EFCC bayan hukumar ta tsare ma'aijin kungiyarsu

- Sai dai yace tun farko an hana shi shiga amma daga bisani aka kira shi ciki kafin a lallasa masa dukan tsiya

Jami'an tsaro dake ofishin hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) sun yi wa shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya, reshen Makurdi, Barista Justin Gbagir mugun duka.

A halin yanzu, Gbagir yana kwance a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Binuwai yana karbar taimakon likitoci, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai a asibitin, Gbagir yace sun samu sabani ne lokacin da yaje ofishin EFCC bayan samun wayar cewa daya daga cikin abokan aikinsa Barista Aver Shima na hannun hukumar.

KU KARANTA: Ku tsammaci sauyi a yanayin ayyukan tsaro, Ministan tsaro ga 'yan Najeriya

Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti
Jami'an EFCC sun yi wa shugaban NBA na Makurdi mugun duka, yana kwance a asibiti. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin sunayen jihohin da zasu fuskanci fari tsakanin Yuni da Augusta, NIMET

"Jiya, Talata 8 ga watan Yunin 2021 wurin karfe 6:59 na yamma, antoni janar kuma kwamishinan shari'a, Michael Gusa Esq, ya kira ni tare da sanar dani cewa ma'aijin kungiyarmu na hannun EFCC.

"Bayan bincike, na gano cewa tana hannun hukumar sakamakon zarginta da ake da baiwa shugaban UBEB shawara wacce daga bisani ya sa hannu kan wata takarda, a yanzu haka EFCC tana bincika.

"Abokiyar aikinmun jami'ar shari'a ce da ma'aikatar shari'a ta jihar Benue kuma an sanyata ne aikin da tayi wa SUBEB."

Yace bayan isarsa ofishin EFCC, ya samu suka daga jami'an tsaro tun a wurin shiga inda suka dinga barazanar harbinsa.

A cewarsa, hakan ta sa shi da sauran abokan aikinsa suka koma gaban wani otal dake kallon hukumar amma sai jami'ai suka ce su bar wurin.

Daga bisani an aiko ya shiga daga cikin inda aka bashi wurin zama amma shugaban ofishin yace bai isa ya zauna ba. Ya tambaya ko matsayin wanda ake zargi yake amma ba a amsa masa ba, haka ta sa ya juya zai fita.

Kamar yadda Gbagir yace, jami'ai wurin bakwai suka biyo shi inda suka dinga dukansa tare da watso shi wajen hukumar.

A wani labari na daban, Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai, ya ce dakatar da Twitter hanya ce ta kawar da hankulan 'yan Najeriya wacce gwamnatin tarayya ta samo domin rufe gazawarta a fannin shawo kan rashin tsaro.

A wata wallafa da yayi a Twitter a ranar Talata, Ortom yace dakatarwan an yi ta ba bisa ka'ida ba inda ya kwatanta lamarin da takura tare da danne hakkin 'yan Najeriya.

Gwamnan jihar Binuwai din ya kara da cewa wannan abu da gwamnati tayi wata hanya ce ta toshe kafafen sada zumuntar zamani, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: