Ku tsammaci sauyi a yanayin ayyukan tsaro, Ministan tsaro ga 'yan Najeriya
- Ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya yace za a ga sauye-sauye a bangaren tsaron kasar nan
- Ya sanar da hakan a ranar Litinin ga manema labaran gidan gwamnati bayan gabatar da sabon COAS Yahaya ga shugaba Buhari
- Magashi yace shugaban kasan ya karba Yahaya inda ya sanar dashi wasu dabaru tare da gogewar da yake da ita a fannin tsaro
Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa za a yi sauye-sauye masu tarin yawa a bangaren yanayin tsaron kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya bada wannan tabbacin ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran gidan gwamnati bayan gabatar da sabon shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
An gabatar da shugaban rundunar sojin kasan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani taro da ya samu halartar shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor.
KU KARANTA: Bidiyon 'yar Najeriya dake siyar da shinkafa dafaffa ta N10, tace tana samun riba
Magashi yace shugaban kasan ya bayyanawa sabon COAS din irin kwarewarsa da dabarun yakin da yake dasu inda ya tunatar dashi halin da tsaron kasar nan ke ciki.
A yayin da aka tambaya abinda shugaban kasan ya sanar da sabon COAS din, ministan ya ce: "Ya sanar da shi cewa akwai damuwa sosai a fannin tsaro kuma yanzu ya bashi dabaru wadanda zamu iya koya daga garesu sannan mu saka su cikin sabbin hanyoyin ayyukanmu.
"Batun hadin kai tsakanin jami'an tsaro an sake jaddada ta kuma ina da tabbacin za a ga sauye-sauye masu tarin yawa a bangaren ayyukan tsaron kasar nan."
KU KARANTA: Dakatar da Twitter a Najeriya zai iya jefamu fatarar kudi, 'Yan kasuwa
A wani labari na daban, sojoji masu mukamin Manjo Janar-janar kuma 'yan aji na 36 na makarantar horar da hafsin soji da aka bayyana za a yi musu ritayar dole bayan nada Manjo Najar Farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa zasu gana da Yahaya tare da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Alhamis.
An tattaro cewa janarorin wadanda suke da ragowar shekaru uku na aiki sun koka da yadda basu zato balle tsammani ake nufo su da batun ritaya.
Sakamakon wannan cigaban, shugaban ma'aikatan tsaro ya gayyacesu wani taro domin su sasanta kan batun a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng