Jerin sunayen jihohin da zasu fuskanci fari tsakanin Yuni da Augusta, NIMET
- NiMet ta bayyana wasu jihohin arewacin Najeriya da zasu fuskanci fari na wani lokaci a shekarar nan
- Jihohin sun hada da Sokoto, Zamfara, Yobe, Kebbi, Katsina, Neja da wasu sassan jihar Borno dake arewa maso gabas
- Kamar yadda Farfesa Matazu ya sanar, yace bayan hakan za a samu ruwa daidai misali a jihohin
Tsananin fari zai shafi jihohin arewacin Najeriya irinsu Sokoto, Zamfara, Yobe, Kebbi, Katsina, Neja da wasu sassan jihar Borno, cibiyar duba yanayi ta Najeriya (NiMet) tace.
Darakta janar na NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya kara da cewa jihohi kamarsu Oyo, Kwara, Ekiti, Filato da birnin tarayya zasu fuskancin farin amma kadan.
KU KARANTA: Dakatar da Twitter a Najeriya zai iya jefamu fatarar kudi, 'Yan kasuwa
KU KARANTA: CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole
Ya sanar da hakan a Abuja bayan sanya hannu a wata takardar yarjejeniya a kan horar da binciken yanayi tsakanin NiMet da jami'ar aikin noma ta Umudike, jihar Abia.
Ya kara da bayyana cewa lamurran yanayi sun nuna cewa jihohin kudu maso gabas da na kudu kudu zasu fuskanci ruwan sama daidai misali amma banda jihar Cross River wacce zata fuskanci ruwa kasa da daidai misali.
Daga watan Yuli zuwa Augusta, darakta janar na NiMet din yace za a fuskanci ruwa daidai misali a jihohin da suka fara fuskantar fari, Daily Trust ta ruwaito.
A yayin bayani kan abinda wannan hasashen zasu iya haifarwa, Farfesa Matazu yace manoma su shuka irin da ya dace domin gujewa muguwar asara. Ya ce manoma su shuka irin da zasu iya jurewa fari.
Ya yi bayanin cewa: "Fari ba rashin ruwa bane, idan aka kwashe kwanaki goma zuwa makonni biyu babu ruwan sama shine farin.
"Dole ne manoma su samu hanyoyin shuka irin da ke jure fari na wani lokaci," ya shawarta.
A wani labari na daban, akwai hasashe tare da rade-radin cewa Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, yana shirin yin murabus daga shugabancin jihar Yobe domin ya samu damar shugabantar jam'iyyar APC, ThisDay ta ruwaito.
Gwamna Buni wanda shine shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya zai kammala wa'adin shugabancin jihar Yobe a karo na biyu a 2023.
Jaridar ta kara da cewa ana tsammanin burin Gwamna Buni ne yasa aka dakatar da sanar da ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.
Asali: Legit.ng