Da duminsa: Twitter ta garzaya wurin FG domin neman sasanci

Da duminsa: Twitter ta garzaya wurin FG domin neman sasanci

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya tabbatar da cewa Twitter ta garzaya wurin gwamnatin tarayya don neman sasanci

- Lai Mohammed ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa

- Kamar yadda yace, tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu saboda rahotannin asarar biliyoyin da Twitter ta tafka cikin kwanakin nan

Gwamnatin tarayya ta ce kamfanin Twitter, ya garzaya domin neman sasanci da gwamnatin Najeriya.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwar ta tarayya.

Ya bayyana cewa tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu saboda an samu rahotanni na gagarumar asarar da twitter ta dinga tafkawa na biliyoyi, Channels Tv ta ruwaito.

KU KARANTA: Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bankado yunkurin safarar jarirai 2

Da duminsa: Twitter ta garzaya wurin FG domin neman sasanci
Da duminsa: Twitter ta garzaya wurin FG domin neman sasanci. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku tsammaci sauyi a yanayin ayyukan tsaro, Ministan tsaro ga 'yan Najeriya

Ministan labarai ya jaddada cewa Twitter kafa ce ta zabi kuma ba za a bar ta ta cigaba da aiki a Najeriya ba har sai tayi rijista, an bata lasisi kuma ta cigaba da aiki kan dokoki.

Yayin da aka tambaya ministan dokar kasar Najeriya da twitter ta karya kuma za a hukuntata, Lai ya ki amsawa sai yace Antoni janar na tarayya ya amsa.

A yayin jawabi game da taron majalisar zartarwa na tarayya da ya samu shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mohammed ya ce a kan dakatarwan ne kuma ya bukaci 'yan siyasa da su jeru a bayan gwamnatin tarayya domin bata goyon baya kan hukuncinta.

A wani labari na daban, Oluwarotimi Agunsoye, dan majalisar wakilai a Najeriya yace gwamnatin ta fadi warwas saboda yadda ta kasa baiwa rayuka da kadarorin 'yan kasa kariya a Najeriya.

Agunsoye dan majalisar ne daga jihar Legas kuma dan jam'iyyar APC mai mulkin ne wanda ya sanar da hakan a zauren majalisar wakilai a ranar Talata.

Yana bada gudumawa kan batutuwan kashe-kashe da ke aukuwa a kwanakin nan cikin kasa, The Cable ta ruwaito.

Tanko Sununu, dan majalisa daga jihar Kebbi ne ya dauka nauyin batun a madadin sauran takwarorinsa na jihar inda ya kushe hatsarin jirgin ruwa da ya lakume rayuka 97 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel