Gwamnati ta fadi warwas a wurin baiwa 'yan Najeriya kariya, Dan majalisar APC

Gwamnati ta fadi warwas a wurin baiwa 'yan Najeriya kariya, Dan majalisar APC

- Dan majalisar wakilai, Oluwarotimi Agunsoya daga jihar Legas yace gwamnati ta fadi warwas

- Kamar yadda dan jam'iyyar APC ya sanar a zauren majalisar, yace gwamnati ta gaza baiwa rayuka kariya

- Ya koka da yadda aka rasa rayuka 97 a Kebbi, sama da 50 a Igangan da kuma sauran sassan kasar nan

Oluwarotimi Agunsoye, dan majalisar wakilai a Najeriya yace gwamnatin ta fadi warwas saboda yadda ta kasa baiwa rayuka da kadarorin 'yan kasa kariya a Najeriya.

Agunsoye dan majalisar ne daga jihar Legas kuma dan jam'iyyar APC mai mulkin ne wanda ya sanar da hakan a zauren majalisar wakilai a ranar Talata.

Yana bada gudumawa kan batutuwan kashe-kashe da ke aukuwa a kwanakin nan cikin kasa, The Cable ta ruwaito.

Tanko Sununu, dan majalisa daga jihar Kebbi ne ya dauka nauyin batun a madadin sauran takwarorinsa na jihar inda ya kushe hatsarin jirgin ruwa da ya lakume rayuka 97 a jihar.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter a Najeriya zai iya jefamu fatarar kudi, 'Yan kasuwa

Gwamnati ta fadi warwas a wurin baiwa 'yan Najeriya kariya, Dan majalisar APC
Gwamnati ta fadi warwas a wurin baiwa 'yan Najeriya kariya, Dan majalisar APC. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole

Muraina Ajibola daga jihar Oyo tare da 'yan majalisa 66 sun bukaci sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da ya tabbatar da damko makasan mutum 50 na garin Igangan dake jihar Oyo.

Agunsoye, wanda ya goyi bayan bukatarsu, ya jajanta yadda dukkan yankuna shida na kasar nan suka zama tamkar filin daga sakamakon rashin tsaro.

"Ya abokan aikina, mutumin da aka fi tsana a duniya shine wanda ke fadin gaskiya kuma jama'a basu son sauraron gaskiya saboda dacinta," yace.

"A gaskiya mun fadi warwas a wannan lamarin. Abokin aikina Sununu yace sama da mutum 70 sun rasa rayukansu. Abokin aikina daga jihar Oyo yace sama da mutum 50 suka rasa. Wani daga Imo yace ana kashe musu mutane. Ku je yankunan arewa maso gabas, arewa ta tsakiya, kudu maso gabas. kudu maso yamma, arewa maso yamma, kudu kudu, jama'armu suna ta mutuwa. Me muke yi a matsayinmu na gwamnati?"

A wani labari na daban, akwai hasashe tare da rade-radin cewa Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, yana shirin yin murabus daga shugabancin jihar Yobe domin ya samu damar shugabantar jam'iyyar APC, ThisDay ta ruwaito.

Gwamna Buni wanda shine shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya zai kammala wa'adin shugabancin jihar Yobe a karo na biyu a 2023.

Jaridar ta kara da cewa ana tsammanin burin Gwamna Buni ne yasa aka dakatar da sanar da ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel