CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole

CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole

- Sojoji 29 da rundunar sojan Najeriya ke shirin yi musu ritaya zasu gana da shugaban ma'aikatan tsaro

- An gano cewa manyan sojojin wadanda suke gaba da COAS Yahaya suna ta guna-guni kan ba-zatan da aka yi musu

- Ana tsammanin bayan sojoji 29, akwai yuwuwar hukumar ta sallami 'yan aji na 37 duk da babu tabbaci a yanzu

Sojoji masu mukamin Manjo Janar-janar kuma 'yan aji na 36 na makarantar horar da hafsin soji da aka bayyana za a yi musu ritayar dole bayan nada Manjo Najar Farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa zasu gana da Yahaya tare da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Alhamis.

An tattaro cewa janarorin wadanda suke da ragowar shekaru uku na aiki sun koka da yadda basu zato balle tsammani ake nufo su da batun ritaya.

Sakamakon wannan cigaban, shugaban ma'aikatan tsaro ya gayyacesu wani taro domin su sasanta kan batun a ranar Alhamis.

KU KARANTA: King of Dragons: Jami'an tsaro a Imo sun sheke hatsabibin shugaban IPOB/ESN

CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole
CDS da COAS zasu gana da hafsoshin soji 29 da za a yi wa ritayar dole. Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dan sanda ya sheka lahira yayin da 'yan bindiga suka kashe manoma 41 a Zamfara

Thisday ta gano cewa wadanda ritayar karfi da yajin ta shafa an bukaci su tafi hutun wata daya na dole

"Ana cigaba da aunawa tare da duba makomar 'yan aji na 36 da 37. Zasu samu ganawa da CDS a ranar Alhamis," majiya daga rundunar sojin tace.

Wata majiya ta ce: "Sun ta damuwa tare da korafi saboda an yi musu ba-zata. Wasu daga cikinsu basu da shirin ritaya saboda suna da sauran shekaru uku kuma a yanzu ne zasu shirya. Amma ga inda suka kare yanzu."

An gano cewa makomar 'yan aji na 37 wadanda sune suka kammala karatu tare da shugaban sojin kasan har yanzu ba a yanketa ba.

Akwai alamun dake nuna za a bukaci su tafi, amma hakan ya dogara da hukuncin hukumar rundunar sojin wanda take samun shugabancin ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya.

A wani labari na daban, Kamfanin Twitter ya nuna shirinsa na taimakon 'yan Najeriya wurin amfani da kafar sada zumuntar duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da hakan.

A wata takarda da ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma'a, ya sanar da dakatarwan inda yace ana amfani da kafar wurin kaskanci tare da muzgunawa Najeriya.

Amma martani da aka yi wa kasar bayan dakatarwan, Twitter ta wallafa cewa zata yi duk abinda ya dace wurin baiwa 'yan Najeriya damar amfani da kafar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng