Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter

Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter

- Gwamnatin tarayya ta musanta rahoton dake yawo na cewa ta bada sharadi kafin ta dage dakatar da Twitter da tayi a kasar nan

- Ferdinand Nwonye, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni a Abuja

- Nwonye ya kara bayanin cewa ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya tattauna da wasu wakilai, ba a fahimci bayaninsa bane

Ma'aikatar harkokin waje a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, ta ce gwamnatin tarayya bata zayyana wasu sharudda ba da za ta saka a dage dakatar da Twitter da aka yi a kasar nan.

Legit.ng ta ruwaito cewa hakan yana kunshe a wata takarda da mai magana da yawun ma'aikatar, Ferdinand Nwonye, ya fitar.

KU KARANTA: Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau har lahira

Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter
Da duminsa: Babu sharadin da FG ta kafa na dage dakatar da Twitter. Hoto daga Ministry of foreign affairs
Asali: UGC

KU KARANTA: Twitter ta sha alwashin ba 'yan Najeriya damar amfani da ita duk da Buhari ya dakatar

Takardar mai taken, "Karin bayani kan tsokacin mai girma ministan harkokin waje a wurin taro da wakilai."

Nwonye yace ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya gana da tawagar Amurka, kungiyar gamayyar Turai, Jamhuriyar Ireland da Canada a ranar Litinin a Abuja a kan tsokacin da yasa gwamnati ta dakatar da Twitter a Najeriya.

Ya kara da cewa abokai biyar sun saka hannu kan wata takarda a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni inda ta kushe dakatar da Twitter a Najeriya tare da kwatanta shi da take hakkin dan Adam.

A wani labari na daban, dakarun sojin kasa na Najeriya sun harbe wani babban kwamandan ESN, kungiyar miyagun 'yan ta'adda dake rajin karbar kasar Biafra a babban birnin jihar Imo, Owerri.

Birgediya Janar Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar a wata takarda ta ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni ta shafinsu na Facebook, ya bayyana sunan kwamandan da aka kashe da Joseph Uka Nnachi, wanda aka fi sani da King Of Dragons.

Yerima ya sanar da cewa dakarun sojin da suka samu tallafin jami'an runduna ta musamman ta 'yan sanda sun halaka Dragon tare da wasu mambobi hudu bayan jami'an tsaro sun fatattaki wadanda suka kaiwa ofishin 'yan sanda hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng