Jami'an DSS suna neman Fasto Mbaka, bayan ya cigaba da caccakar Gwamnatin Buhari a mimbari

Jami'an DSS suna neman Fasto Mbaka, bayan ya cigaba da caccakar Gwamnatin Buhari a mimbari

- Ejike Mbaka ya ce jami’an DSS sun duro gidansa, sun gayyace shi zuwa Abuja

- Faston ya ce a lokacin da aka kawo masa takardar gayyatar a Enugu, ba ya gida

- Mbaka ya koka a kan halin da kasa ta ke ciki, duk da an hana shi yin magana

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron DSS masu fararen kaya suna neman limamin cocin Adoration Ministries da ke garin Enugu, Fasto Ejike Mbaka.

A ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni, 2021, Faston ya bada labari da bakinsa cewa wasu jami’an DSS sun ajiye masa takarda a gidansa, ana gayyatarsa zuwa Abuja.

Jaridar The Cable ta ce jami’an tsaron sun zo gidan malamin addinin a garin Enugu, suka nemi ya hallara a birnin tarayya, ana tunanin zai amsa wasu tambayoyi.

KU KARANTA: Ba mu dauke Fasto Mbaka ba, inji DSS

Da yake magana a wajen hudubarsa ta makon da ya gabata, Faston katolikan ya ce mutanen da ke gidansa ba su karbi takardar gayyatar da DSS suka aiko masa ba.

“A ranar Alhamis da safe, an kira daga inda na ke cewa jami’an DSS sun zo daga Abuja, suna kofar gida na, suna gayyata ta zuwa garin Abuja. Saboda mene?”

Ya ce: “Abin da na gagara fahimta shi ne ka da ayi gigin tankwarar da coci, wurin ibada.” The Guardian ta ce ya sha alwashi ba zai daina fadar gaskiya ba.

Ejike Mbaka ya ce ba za ayi nasara wajen taba malamai da jami’an tsaron da su ke kokarin yi ba. Faston ya ce masu gadin gidansa ba su bari sun karbi takardar ba.

KU KARANTA: Ministan sadarwa ya lashe lambar yabon Blueprint na 2020

Jami'an DSS suna neman Fasto Mbaka, bayan ya cigaba da caccakar Gwamnatin Buhari a mimbari
Jami'an DSS da Fasto Mbaka Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Shehin addinin kiristan ya tabo halin da ake ciki akasa, ya ce miliyoyin matasa ba su da aikin yi, ya ce a matsayinsa na uba, ba zai yi shiru alhali ana shan wahala ba.

Ya ce: "annan shi ne Mbaka da ya yi aiki da Eneja, ya soki Abacha da sauransu, ya je Minna ya fadawa Babangida, ya yi ido biyu da Obasanjo, ya fada masa gaskiya.”

Da aka nemi jin ta bakin DSS ta hannun mai magana da yawunta, Peter Afunanya, bai ce uffan ba.

Wannan gayyata ta na zuwa ne bayan an ji babban limamin cocin na Adoration Ministries Enugu Nigeria, AMEN, ya na cewa ya kamata shugaban kasa ya yi murabus.

Lamarin har ya kai kwanakin baya aka yi ta rade-radin DSS ta kama Malamin. Kwatsam sai aka ga Ejike Mbaka, ya sake bayyana, aka kawo karshen wannan jita-jitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng