Magoya bayan Atiku sun yi sammako, sun fara yi masu yakin neman Shugaban kasa tun yanzu

Magoya bayan Atiku sun yi sammako, sun fara yi masu yakin neman Shugaban kasa tun yanzu

- Wasu sun kaddamar da shirin yakin neman zaben Atiku Abubakar/Charles Soludo

- APGA Movement for a United Nigeria ta na so PDP da APGA su hada-kai a 2023

- Kungiyar ta ce idan PDP ta hada-kai da tsohon Gwamnan na CBN, za ta kai labari

Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar da Charles Soludo sun kaddamar da yakin neman zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce magoya bayan Atiku Abubakar da Farfesa Charles Soludo sun soma yi masu fafatukar zaba shugaban kasa a 2023.

Wajen kaddamar da wannan shiri a yau, 7 ga watan Yuni, 2021, a garin Abuja, shugaban tafiyar, Kwamred Andy Ekwe, ya bayyana manufarsu.

KU KARANTA: Jerin shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36

Yayin da Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shuugaban kasa ne kuma jigo a PDP, Charles Soludo ba ya tare da jam’iyyarsa.

Tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya, Farfesa Charles Soludo, ‘dan jam’iyyar APGA ne, kuma ya taba takarar gwamnan jihar Anambra.

Andy Ekwe da kungiyarsa ta APGA Movement for a United Nigeria sun ce Atiku da Soludo ne mafita idan ana so a fita daga halin da ake ciki.

Ekwe yake cewa ya zama dole ‘Yan Najeriya su bi tafiyarsu domin ceci kasar nan daga halin da aka shiga na zalunci, tashin-tashina, da rashin tsaro.

KU KARANTA: Zabe mai zuwa na mai rabo ne ba 'Yan Kudu ba– Sanatan Bauchi

Magoya bayan Atiku sun yi sammako, sun fara yi masu yakin neman Shugaban kasa tun yanzu
Atiku Abubakar Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

"Fafutukarmu ita ce ganin APGA ta ba Soludo tikiti ta yadda zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku domin su karbi mulki."

“Mun samu damar kaddamar da shirin neman zabe na hadin-gwiwar, Atiku da Soludo.” Punch ta rahoto bangaren Atiku ta na cewa babu hannun ta.

APGA Movement for a United Nigeria ta ce gamayyar PDP da APGA zai kawo nasara, har ya zarce kokarin da APP da AD su ka yi a zaben da aka yi 1999.

A yau ne aka ji cewa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega ya caccaki Shugabannin Najeriya, ya ce ba su san inda suka dosa ba.

Masanin harkar siyasar ya ce babu abin da ke gaban masu mulki sai son-kai da ‘dan karen kwadayi da handamar dukiyar al'umma, babu kishi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel