Hotunan Makarantar Sakandare Na Chibok Da Zulum Ya Sake Ginawa

Hotunan Makarantar Sakandare Na Chibok Da Zulum Ya Sake Ginawa

- Ministan Harkokin Mata, Pauline Tallen ta kaddamar da sabon ginin makarantar sakandare ta mata a Chibok, jihar Borno

- Gwamna Babagna Zulum na jihar Borno ne ya sake ginin makarantar kimanin shekaru bakwai bayan sace yan mata a makarantar

- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin samar da na'urar wutar lankarki mai aiki da hasken rana da wasu kayayaki a makarantar

Pauline Tallen, Ministan Harkokin Mata, a ranar Litinin, ta kaddamar da ginin sabon makarantar sakandare na mata ta Chibok da ke jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014, yan ta'addan Boko Haram sun kutsa makarantar sun sace dalibai mata 276 da ke shirin rubuta jarrabawar su na karshe.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Hukumar Yan Sanda Ta Dakatar Da Bada Izinin Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu

A cikinsu, 164 sun tsere, an sako su ko an gano su amma kawo yanzu bayan shekaru bakwai, 112 cikin yan matan suna nan tare da yan ta'addan.

A watan Nuwamban 2020, Gwamna Babagana Zulum na jihar, ya sake gyara makarantar.

Da ya ke magana wurin kaddamarwar, Tallen ta ce sake gina makarantar ya nuna zaman lafiya ya dawo garin Chibok, ta kuma bukaci mazauna garin kada su karaya saboda abin da ya faru a 2014.

Yayin da ta ke jinjinawa Zulum saboda sake gina makarantar, ministan ta sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta saka na'urar bada lantarki da rana wato sola guda 50 da wasu kayayaki a makarantar.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Ɗauki Sabbin Ma'aikata '10,000' a Yayin Da Jihar Ke Rage Ma'aikata

A jawabinsa, gwamnan ya ambaci wasu abubuwan cigaba da aka samu yana mai cewa gwammatinsa za ta cigaba da aiki don habbaka jihar.

Ga hotunan a kasa:

Hotunan Makarantar Sakandare Na Chibok Da Zulum Ya Sake Ginawa
Hotunan Makarantar Sakandare Na Chibok Da Zulum Ya Sake Ginawa. Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: