Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce

Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce

- Kamar yadda Twitter ta cire wallafar shugaban kasa Buhari, Facebook ta bi ayari inda ta cire a yau Juma'a

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kakkausan jan kunne ga masu tada kayar baya na IPOB inda yace basu san yakin basasa ba

- Sai dai kafar sada zumuntar ta Facebook tace wallafar ta take dokokinta na duniya, don haka ta sauke wallafar

Facebook, wata kafar sada zumuntar zamani ta cire tsokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafinsa.

Shugaban kasan a ranar Talata yayi barazanar maganin masu kai farmaki ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta kamar yadda sojoji suka yi wa 'yan tawaye a yakin basasa.

Buhari, soja mai mukamin janar amma wanda yayi ritaya ya yi yakin basasa wanda ya lamushe rayukan sama da mutum miliyan daya, Premium Times ta ruwaito.

"Da yawa daga cikin wadanda ke rashin da'a a yau yara ne da basu san barnar kadarori da rayukan da aka yi ba yayin yakin basasa. Mu da muka yi watanni 30 a filin daga, muka ga yakin basasa, zamu yi muku magana a yaren da kuke fahimta," yace.

KU KARANTA: Hotunan miyagun makamai da aka samu bayan sojoji sun sheke dillalan makamai 3 a Sokoto

Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce
Da duminsa: Bayan Twitter, Facebook ta goge tsokacin Buhari kan yakin basasa da ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan hasashen ritayar dole ga manyan sojoji

Amma a ranar Juma'a, bayan rahoton da ma'abota Facebook suka dinga kaiwa, Facebook ta cire wallafar daga kafar.

"Duba da dokokinmu na duniya, mun cire wallafar da shugaban kasa Buhari yayi a shafinsa na Facebook bayan karya dokokinmu na hana tada tarzoma. Muna cire duk wata wallafa ta mutum ko kungiya da ta take dokokin Facebook," kafar tace.

Duk da a halin yanzu babu wallafar a shafin Buhari, har yanzu yana nan a na hadiminsa Femi Adesina.

Har yanzu babu tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta dakatar da aiki da Facebook kamar yadda tayi da Twitter a yau.

A wani labari na daban, an tabbatar da kisan 'yan bindiga biyar a yammacin Laraba yayin da suka yi arangama da rundunar 'yan sanda a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan da zasu kai dari da hamsin sun tsinkayi kauyukan Wurma da Yarbudu, jaridar ThisDayLive ta ruwaito.

Amma kuma 'yan sandan dake kauyen Wurma sun yi gaba da gaba da 'yan bindigan. Majiya daga rundunar 'yan sandan tace daya daga cikin 'yan bindigan ya sheka lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel