Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas

Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas

- 'Yan sandan jihar Ribas sun tabbatar da cafke wasu 'yan fashi da makami uku da suka addabi jihar Ribas

- Dubun 'yan fashin ta cika ne bayan da suka tare wani mutum mai suna Simon Ibrahim yayin da yake hanyar kai kudi banki

- Rundunar 'yan sandan tace Simon ne ya kira su kuma suka kai dauki tare da cafke miyagun uku kuma an fara bincike

Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta cafke wata kungiyar 'yan fashi da makami ta mutum uku da suka kware wurin fashi ga jama'a a wuraren Choba/Obiri dake Ikwerre a jihar.

An kama su ne bayan nasarar da suka samu wurin fashi ga wani Simon Ibrahim wanda ke kan hanyarsa ta zuwa banki zuba kudi. Kungiyar ta tare shi yayin da yake tuka motarsa kirar Mazda.

Amma kuma sa'a ta kubuce musu yayin da wanda suka tare din ya kira 'yan sanda kuma aka kama su a take tare da kaisu ofishin 'yan sanda dake Choba, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun sheke mayakan ISWAP, sun lalata musu motocin yaki 6 a Borno

Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas
Gagararriyar kungiyar fashi da makami ta mutum 3 ta shiga hannun 'yan sanda a Ribas. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bishop Kuka yayi kira ga shugabannin Najeriya da su daina daukar rantsuwar da basu kiyayewa

Rundunar 'yan sandan tace ana cigaba da bincikar wadanda aka kama kuma za a mika su kotu bayan an kammala dukkan binciken.

A wani labari na daban, shugaban sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jinjinawa kokarin dakarun sojin kasan Najeriya dake aiki wurin Sabon Birni, garin da ke iyakar jihar Sokoto.

Dakarun sojin sun yi musayar wuta da wasu da ake zargin dillalan bindigogi ne kuma sun kashe mutum ukun tare da samo miyagun makamai daga wurinsu.

Wannan jinjinar na dauke ne a wata takarda da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya wallafa a Twitter sannan ya mika ga manema labarai.

Kamar yadda Yerima yace, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri ne a kan kaiwa da kawowar dillalan bindigogin daga jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya kuma cike da nasara suka bibiyi wadanda ake zargi.

Babu kunya balle tsoro wadanda ake zargin suka fara sakarwa dakarun harbi, a take kuwa sojojin suka mayar da martani, lamarin da yasa aka kashe mutum uku a cikin wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel