Bidiyon mutumin da ya dako tsalle daga jirgin sama babu kumbo, ya kafa tarihi a duniya
- Wani shahararren matukin jirgin sama ya kafa tarihi a duniya bayan ya dako tsalle na tsayin mita 7620 daga jirgi ba tare da kumbo ba
- Wanda ya kafa tarihin mai suna Luke Aikins a wani bidiyo ya gigita jama'a a kafar sada zumunta ta yanar gizo bayan saukowa da yayi daga jirgi
- Wannan lamari kuwa ya baiwa jama'a mamaki da wasu tunane-tunane daban-daban daga jama'a a kafafen sada zumunta
AirLive ta tabbatar da yadda wani matukin jirgin sama mai suna Luke Aikins ya kafa tarihin duniya inda ya zamo wanda ya taba dirkowa daga wuri mafi nisa ba tare da kumbo ba.
Mutumin a wani bidiyo da @PriapusIQ ya wallafa a Twitter, an ga yadda ya dako tsalle daga jirgi wanda yake da nisan mita 7620 kuma ya sauka babu taimakon kumbo.
KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5
A bidiyon da tuni ya yadu, an ga Aikins tare da wasu mutane uku wadanda suke taya shi aiwatar da manufarsa wacce ta sa ya kafa tarihi.
Wannan abinda yayi kuwa ya janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafar sada zumunta da suka kalla bidiyon.
@EllinoeLessetti cewa yayi: "Ina da tabbacin wadanda suka fado ba tare da sun so ba sun kafa tarihin da yafi wannan na fadowa daga jirgin sama ba tare da kumbo ba kuma suka rayu."
@JP__z rubutawa yayi: "Wannan abu ya kayatar da ni. Ka kwatanta haifo ka da aka yi a titin Indiya ba tare da wani abun arziki ba, kawai sai wata rana ka ga wani ya fado daga jirgi babu kumbo. Abun akwai kayatarwa."
@mtb4misoul martani yayi da cewa: "Babbar raga... Abun bai kayatar da ni ba. Ka sauka da kafafunka idan kana son mutuntawa ta."
A wani labari na daban, jami'an tsaron hadin guiwa (JTF) sun damke jama'a masu yawa masu alaka da kashe-kashen jami'an tsaro a kananan hukumomin Essien udim, Oboto Akara da Ikot Ekpene dake jihar Akwa Ibom.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kamen ya biyo bayan jerin samamen da JTF din da suka hada sojoji, 'yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC ke kaiwa wurare daban-daban da suka zama maboyar 'yan ta'adda a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Andrew Amiengheme, a wata takardar da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa JTF din sun samo ababen hawa da makamai daga wadanda ake zargin.
Asali: Legit.ng