Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan hasashen ritayar dole ga manyan sojoji
- Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta rade-radin dake yawo na cewa za a yi kakkabar manyan janarori a rundunar soji
- Kamar yadda daraktan yada labaran tsaro, Bernard Onyeuko ya sanar, yace zance ne mara tushe balle makama
- Ya kara da tabbatar da cewa babu wani hafsan soja da hukumar ta amince yayi murabus ballantana da kanta ta yi masa ritaya
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce rade-radin da ake na cewa akwai yuwuwar ritayar wasu sojoji masu mukamin janar-janar bayan nadin da shugaban kasa yayi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa, ba gaskiya bane.
Mukaddashin daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja a ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.
Onyeuku yace murabus din wasu manyan hafsoshin sojoji a rundunar na sa kai ne, kari da cewa har yanzu rundunar bata aminta da ritayar wani hafsan soja ba.
KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5
"A wannan lokacin, dukkanku kun san nadin da aka yi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.
"Wannan ya janyo rade-radi daga kafafen yada labarai akan yadda za a kakkabe wasu manya a rundunar.
“Ina so in yi amfani da wannan damar wurin musanta rade-radin nan marasa tushe domin kuwa murabus ga hafsan soja sa kai ne ga wadanda suka so.
"Ina sake tabbatar da cewa babu wani murabus din hafsan soja da hukumar ta aminta da shi," yace.
A wani labari na daban, Twitter ta yi bayanin dalilinta na goge wallafar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kafar sada zumuntar, lamarin da ya kawo cece-kuce daga 'yan Najeriya.
Wallafar wacce take daga cikin wallafofin da Buhari yayi a ranar Talata ta ce: "Da yawa daga cikin masu rashin da'a a yau basu da wayon sanin asara da rashin rayuka da aka yi yayin yakin basasa.
"Mu da muke filin daga na watannin 30, muka ga yaki, za mu yi musu magana da yaren da muka san zasu gane."
Asali: Legit.ng