'Karin Bayani: Sojan Da Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Legas Ya Kashe Kansa

'Karin Bayani: Sojan Da Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Legas Ya Kashe Kansa

- Wani sojan Nigeria ya bindige jami'in hukumar kwastam har lahira a garin Seme da ke Legas

- Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce mutane sunyi matukar mamakin ganin sojan ya aikata hakan har suna zargin yana cikin mayen gida ne

- Mai magana da yawun hukumar kwastam, Abdullahi Hussain, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce sojan ya halaka kansa daga bisani

Wani soja ya bindige jami'an kwastam har lahira a kan iyakar Seme Borde da ke jihar Legas.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a daren jiya Laraba.

Da Duminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border
Da Duminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border
Asali: Original

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Shaidan ganin idon ya ce kada a ambaci sunansa ya ce lamarin ya bawa mutane da dama mamaki.

"Akwai yiwuwar sojan ya bugu da giya ne domin babu wanda ya taba tsammanin zai aikata irin wannan lamarin," in ji shi.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'

Seme gari na a Nigeria da ke da iyaka da Cotonou, babban birnin Jamhuriyar Benin.

Abdullahi Hussain, Mai magana da yawun hukumar kwastam ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa sojan ya halaka kansa bayan kashe jami'in na kwastam.

Ya ce an fara gudunar da bincike a kan lamarin.

Wakilin Daily Trust wanda ya ziyarci garin na Seme wadda ke da iyak da Kwatano, babban birnin Jamhuriyar Benin ya ga sojoji masu yawa a garin.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel