An Kama 'Yan IPOB Da Suka Kashe 'Yan Sanda a Jihar Akwa Ibom

An Kama 'Yan IPOB Da Suka Kashe 'Yan Sanda a Jihar Akwa Ibom

- Rundunar sojojin Nigeria ta ce ta kama wasu yan IPOB da ke da hannu wurin kaiwa jami'an tsaro hari a Akwa Ibom

- Bernard Onyeuko, mukadashin kakakin soja ya ce bayannan sirri ya nuna wadanda aka kama na da hannu a kisa da kona yan sanda

- Onyeuko ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa yan jarida bayanin nasarorin da rundunar ta samu a watannin Mayu da farkon Yuni

Hedkwatar Tsaro ta Sojojin Nigeria ta ce an kama wasu daga cikin mambobin kungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB) 'da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda a Akwa Ibom, The Cable ta ruwaito.

Akwa Ibom na daya daga cikin jihohin kudancin Nigeria inda ake kaiwa jami'an tsaro a watannin baya-bayan nan.

An Kama 'Yan IPOB Da Suka Kashe 'Yan Sanda a Jihar Akwa Ibom
An Kama 'Yan IPOB Da Suka Kashe 'Yan Sanda a Jihar Akwa Ibom. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border

Hare-haren sunyi sanadin salwantar rayyukan jami'an tsaro 11 a cikin watanni uku da suka gabata.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan, sashin watsa labarai na sojoji, ya ce sojoji sun fara yi wa miyagun dauki dai-dai.

Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Onyeuko ya ce, "bayyanan sirri masu inganci sun bawa sojoji damar kamo mambobin IPOB/ESN" wadanda aka ce sune suke kai wa jami'an tsaro hare-hare a jihar.

"Sojoji a Ikot Ekpene sun kama wasu mambobin IPOB/ESN a karamar hukumar Essien Udim a Akwa Ibom bayan samun bayannan sirri kan ayyukansu a yankin," in ji kakakin na sojoji.

"Wadanda ake zargin suna daga cikin mambobin IPOB/ESN da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda da ofisoshin yan sanda a yankin."

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel