Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya a Neja Zasu Ƙara Ƙudin Fansa

Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya a Neja Zasu Ƙara Ƙudin Fansa

- Yan bindigan da suka sace ɗaliban islamiyya a jihar Neja sun yi barazanar ƙara kuɗin fansa daga miliyan N110m

- Sun ce matuƙar aka gaza biyan su abinda suka nema kafin ranar Laraba to zasu ƙara yawan kuɗin

- Shugaban makarantar, Malam Abubakar Alhassan, shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi

Yan bindigan da duka sace ɗalibai a makarantar islamiyya dake Tegina, ƙaramar Hukumar Rafi, sun yi barazanar zasu ƙara kuɗin fansa daga miliyan N110m da suka nema a farko, kamar yadda thisday ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Yan bindigan sun ce zasu ƙara kuɗin matuƙar ba'a biya yadda suka nema kafin jiya Laraba ba.

Shugaban makarantar, Abubakar Alhassan, wanda shine ya tattauna da yan bindigan, yace buƙatar su ta sanya yan garin cikin ruɗani.

Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya a Neja Zasu Ƙara Ƙudin Fansa
Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya a Neja Zasu Ƙara Ƙudin Fansa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Alhassan ya bayyana cewa Sun sace malamai mata guda biyu, inda suka tilasta wa ɗaya ta bada lambar wayar shugaban.

A cewar Alhassan: "Yan bindigan sun kira shi a waya sun nemi a biya su miliyan N300m kafin su saki ɗaliban, na faɗa musu bamu da wannan maƙudan kuɗin, sai suka rage zuwa miliyan N110m amma da sharadin zasu ƙara kuɗin idan ba'a biya kafin jiya Laraba ba."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

Legit.ng hausa ta gano cewa gwamnatin jihar Neja ta tuntubi shugaban makarantar.

Alhassan yace: "Sakataren gwamnati ya tuntuɓe ni ta hanyar matar gwamna saboda ance gwamnan bayanan. Matar gwamnan ta kira ni, ta haɗa ni da sakataren gwamnatin inda yayi alƙawarin gwamnati zata shiga cikin lamarin."

Shugaban makarantar, Malam Abubakar Alhassan, ya jaddada cewa sun tabbatar da ɗalibai 150 ne yan bindigan suka sace.

A wani labarin kuma Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel