'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Rugar Fulani a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Rugar Fulani a Jihar Zamfara

- Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wani rugar fulani da ke Anka a jihar Zamfara

- Sai dai jami'an tsaro da aka tura garin sun fatattake su sun kwato shanun da suka sace

- Kwamishinan yan sandan Zamfara ya yabawa jami'an tsaro ya umurci mutane su cigaba da basu hadin kai

Yan bindiga sun kai hari a wani rugar Fulani da ke wajen garin Anka a hanyar Bagega zuwa Anka a jihar Zamfara.

Majiyoyi sun shaidawa Channels Television cewa yan bindigan sun kutsa garin misalin karfe 5 na yamma suka fara harbe-harbe ba tare da kakautawa ba.

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Rugar Fulani a Jihar Zamfara
'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Rugar Fulani a Jihar Zamfara. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

Sai dai jami'an yan sanda da aka ajiye a wani kamfanin hakar ma'adinai da ke kan hanyar sun tunkari yan bindigan inda suka yi musayar wuta kamar yadda wani ganau ya bayyana a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Ya ce ba a rasa rai sakamakon harin ba amma yan bindigan sun sace shanu da a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba daga mazauna garin.

Shaidan ganin idon ya kuma ce yan bindigan sun kona babur din sarkin Fulanin Anka.

Rundunar yan sandan a jihar ta tabbatar da harin tana mai cewa yan sandan sun dakile harin sannan sun kwato shanun da yan bindigan suka sace.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin yan sandan jihar, Shehu Mohammed ya yi bayanin cewa an sanar da yan sandan da aka tura Anka cewa yan bindiga sun kai hari.

"Hadakar yan sanda da sojoji da aka tura wurin sunyi musayar wuta da yan bindigan.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border

"Sakamakon hakan yan bindigan sun tsere sun shiga daji da raunin bindiga," in ji Mohammed.

Ya kara da cewa, "An kwato dukkan shanun da suka sace a wurin fulanin garin sannan ana cigaba da sintiri domin kare afkuwar wani harin."

Kwamishinan yan sandan jihar, Hussaini Rabiu ya yabawa jami'an tsaron ya kuma yi kira ga jama'a su cigaba da bawa jami'an tsaron hadin kai.

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164