Jami’an Kashe Wuta Sun Ceto Rayuwar Mutum 197 da Dukiyoyin Miliyan N75m a Jihar Kano

Jami’an Kashe Wuta Sun Ceto Rayuwar Mutum 197 da Dukiyoyin Miliyan N75m a Jihar Kano

- Hukumar kashe wuta ta jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar ceto rayukan mutane 197 a watan Mayu

- Tace ta kuma ceto dukiyoyi na kimanin miliyan N75m a lamarin kashe wuta 68 da ta samu a faɗin jihar

- Kakakin hukumar, Aminu Abdullahi, shine ya faɗi haka, yace mutum 22 sun rasa rayuwarsu

Hukumar kashe wuta ta jihar Kano tace ta ceto rayukan mutum 197 da kuma dukiyoyi na kimanin miliyan N75m a wurin kashe wuta 68 a jihar Kano.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

Hukumar tace ta samu wannan nasara ne a cikin watan Mayu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin hukumar na jihar, Aminu Abdullahi, shine ya bayyana wannan adadin a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Kano, kamar yadda Pm news ta ruwaito.

Jami’an Kashe Wuta Sun Ceto Rayuwar Mutum 197 da Dukiyoyin Miliyan N75m a Jihar Kano
Jami’an Kashe Wuta Sun Ceto Rayuwar Mutum 197 da Dukiyoyin Miliyan N75m a Jihar Kano Hoto: @fedfireng
Asali: Twitter

Hakanan kuma, kakakin hukumar ya ƙara da cewa mutum 22 sun rasa rayukansu, kuma dukiyoyin da suka kai na Miliyan N22.9m sun salwanta a lamarin tashin gobara a jihar.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Yace: "A cikin watan Mayu da ya gabata, jami'an mu sun samu nasarar ceto rayukan mutum 197 a lamarin tashin gobara 68, sun ceto dukiya ta kimanin miliyan N75m."

"Mutum 22 sun rasa rayukansu, hakanan dukiyoyi na kimanin Miliyan N22.9m sun salwanta a cikin wannan lokacin."

"Jami'ai sun yi ƙoƙarin kai agaji a kiran neman ɗauki 84 da muka samu a watan Mayu, amma daga cikinsu akwai 14 wanda kiran ƙarya ne."

A Wani labarin kuma Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa.

Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel