Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos

Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos

- Rundunar 'yan sandan Najeriya sun tabbatar da bankado wani kamfani dake hada AK-47 a Filato

- Kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya sanar, yace an kama mamallakan kamfanin tare da wasu mutum 79

- Frank Mba yace abun takaici ne yadda suke hada bindigogin da sai kwararru zasu iya banbancesu da na Turai

Rundunar 'yan sandan Najeriya tace ta bankado wani wurin hada bindigogi AK-47 a karamar hukumar Jos ta kudu dake jihar Filato a ranar Laraba.

Mai magana da yawun rundunar, CP Frank Mba a Abuja yace sun cafke wasu mutane biyu masu matsakaitan shekaru masu suna Joe Michael da Iliya Bulus a kan laifin mallakar wurin tare da wasu wadanda ake zargi har 79.

Wadanda ake zargin kamar yadda Mba yace, an kama su da taimakon rundunar IRT da ta STS na hukumar 'yan sandan, The Nation ta ruwaito.

Sauran ana zarginsu da laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, hadawa tare da rarraba lambobin mota na bogi.

KU KARANTA: EFCC ta cigaba da garkame katafaren gidajen hadimin NSA Monguno a Abuja

Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos
Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

KU KARANTA: Ganduje ya nada Daraktan Kannywood Ishaq Sidi Ishaq mai bashi shawara

A yayin jawabi ga manema labari bayan damke wadanda ake zargin, Mba ya nuna damuwarsa yadda bindigogin ke cigaba da zama makamai kuma zabin 'yan ta'addan dake addabar kasar nan. Hakan kuwa yana nuna babban matsala ne ga tsaron kasar nan idan ba a shawo kai ba.

Mba ya jajanta yadda kamfanin ke hada bindigogin da sai kwararru ke iya banbancesu da wadanda aka yi a Turai.

Ya bayyana cewa a yayin samamen, an samu bindigogi 20 a kamfani kuma an dade ana bibiyar wadanda ake zargin kafin dubunsu ta cika.

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka'ida ba ga hukumar 'yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka'ida ba a take, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel