Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5

Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5

- 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan jihar Osun kuma sun halaka rayuka biyar

- Kamar yadda aka gano, sun fara da kaiwa wani banki farmaki wurin karfe 3 na yammaci

- Sun karasa wani yankin inda suka dinga harbe-harbe tare da kashe jama'a a wurin cire kudi

Wasu miyagu dauke da makamai sun kai farmaki yankunan Ikire da Apomu dake kananan hukumoniin Irewole da Isokan na jihar Osun kuma ana zargin har sun kashe mutum biyar a Ikire.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, 'yan fashi da makamin sun yi wa wani banki fashi a garin Apomu wurin karfe 3 na yamma kafin su karasa Ikire inda suka kashe mutum uku wuin cire kudi.

KU KARANTA: Ganduje ya nada Daraktan Kannywood Ishaq Sidi Ishaq mai bashi shawara

Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5
Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki yankunan Osun, sun sheke mutum 5
Asali: Original

KU KARANTA: Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka

Hakazalika, wasu mutum biyu sun rasu a yankin sakamakon harbin da 'yan fashin suka dinga yi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tace ba za ta iya cewa ga yawan wadanda suka rasu ba.

Amma ta tabbatar da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Olawale Olokode na wurin da abun ya faru a halin yanzu..

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna kai farmaki sansanin sojoji dake yankin kudancin Borno, kamar yadda majiyoyin tsaro suka sanar.

Kungiyar miyagun 'yan ta'addan sun tsinkayi garin Damboa wurin karfe 10:30 na safe da motocin yaki masu yawa, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya saka jama'ar garin cikin dimuwa yayin da mazauna garin da 'yan gudun hijira ke gudun ceton rayukansu. Kamar yadda majiyar tace, tuni dakarun sojin sama suka garzaya ta jiragen yaki domin baiwa sojojin da 'yan sa kai taimako.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel