Da duminsa: ISWAP suna kai hari sansanin sojoji a jihar Borno, jama'a na gudun ceton rai

Da duminsa: ISWAP suna kai hari sansanin sojoji a jihar Borno, jama'a na gudun ceton rai

- 'Yan ta'addan ISWAP sun kai farmaki sansanin sojojin Najeriya dake Damboa a jihar Borno

- Sun isa garin mai nisan kilomita 100 daga Maiduguri a kan motocin yaki inda suke ta harbi

- Tuni mazauna garin suka fara gudun ceton rai yayin da sojojin sama suke kaiwa na kasa dauki

'Yan bindiga da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna kai farmaki sansanin sojoji dake yankin kudancin Borno, kamar yadda majiyoyin tsaro suka sanar.

Kungiyar miyagun 'yan ta'addan sun tsinkayi garin Damboa wurin karfe 10:30 na safe da motocin yaki masu yawa, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya saka jama'ar garin cikin dimuwa yayin da mazauna garin da 'yan gudun hijira ke gudun ceton rayukansu.

Kamar yadda majiyar tace, tuni dakarun sojin sama suka garzaya ta jiragen yaki domin baiwa sojojin da 'yan sa kai taimako.

KU KARANTA: Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

Da duminsa: ISWAP suna kai hari sansanin sojoji a jihar Borno, jama'a na gudun ceton rai
Da duminsa: ISWAP suna kai hari sansanin sojoji a jihar Borno, jama'a na gudun ceton rai. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja

"Zan iya tabbatar muku da cewa mayakan ISWAP a halin yanzu sun kai hari garin Damboa. Sojojin sama ne ke taimakawa dakarun sojin kasan. A halin yanzu an shawo kan komai," majiyar tsaron ta tabbatar.

Damboa gari ne dake da nisan 100 daga Maiduguri, garin ne kuma cibiyar ta'addanci.

Tun bayan labarin mutuwar Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram, masana lamarin da ya shafi tsaro ke nuna damuwarsu kan halin da tsaron yankin zai kasance.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa na jihar.

Kamar yadda takardar da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya fitar a ranar Litinin ta nuna, gwamnan ya bukaci dukkan kwamishinoni da masu mukaman siyasa na jihar da su koma gida su huta.

Kamar yadda wasikar da Zailani Bappa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana, gwamnan yace wannan sallamar bata shafi duk wata hukumar da kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya kafa ba a jihar.

"Dr Bello Mohammed, Matawallen Maradun, Barden Hausa kuma Shettiman Sakkwato a yau 31 ga watan Mayun 2021 ya rushe majalisar zartarwa ta jihar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel