Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno

- Sojoji bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin wani abu mai fashewa a Borno

- An gano cewa 'yan ta'addan Boko Haram ne suka dasa abun da ya fashe ya kawo wannan ibtila'in

- Wani hafsan soja mai mukamin kanal tare da sojoji hudu sun samu miyagun raunika a harin

A kalla sojoji bakwai na rundunar sojin kasan Najeriya ne suka rasu bayan wani abu mai fashewa wanda 'yan ta'addan Boko Haram suka dasa ya fashe a jihar Borno, Premium Times ta ruwaito.

Wannan harin ya zo kasa da mako daya bayan nada sabon shugaban sojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya.

An nada Yahaya a ranar Alhamis da ta gabata bayan mutuwar tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama.

Kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, babban hafsan soja da wasu kananan sojoji hudu sun samu miyagun raunika sakamakon fashewar abun.

KU KARANTA: Buhari yayi martani kan kisan Ahmed Gulak, ya bayyana matakin dauka

Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno
Abu mai Fashewa ya Tashi da Sojojin Najeriya, 7 sun Sheka Lahira a Borno. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: ECOWAS ta dakatar da kasar Mali saboda yin juyin mulki sau 2 a wata 9

Lamarin da ya faru wurin karfe 10:15 na safiyar Litinin, yana daya daga cikin miyagun tarkon da 'yan ta'addan ke amfani dashi wurin kashe sojoji, wata majiyar tsaro ta tabbatar.

Babban sojan mai mukamin kanal wanda aka boye sunansa, yana kan hanyarsa daga Marti, wani gari dake jihar tare da wasu sojoji 11 dake kan motocin yaki.

Sojojin da suka samu ranika a halin yanzu an garzaya dasu asibitin sojoji dake Maiduguri.

A wani labari na daban, Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, yace naira tana halin da yafi dacewa da ita duba da halin da muke ciki.

A ranar Alhamis da ta gabata, naira ta kara daraja da kashi 0.1 inda ta koma N411 daidai da $1 amma kuma ta rage daraja da kashi 0.4 a kasuwar tsaye inda ta koma N495 daidai da $1.

A yayin jawabi a shirin siyasa na ranar Lahadi da gidan talabijin na Channels, Shehu yace kusan shekara daya da ta gabata, annobar korona ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

Mai magana da yawun shugaban kasan yayi ikirarin cewa tattalin arzikin Najeriya ne kadai a Afrika yake ta habaka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel