Fusatattun matasa sun kori basarake daga fadarsa bayan mutuwar dan sanda a yankin
- Fusatattun matasa sun fatattaki basarake Oba Idowu Faborade daga fadarsa bayan mutuwar wani dan sanda a yankin
- Dan sandan mai kula da sashin yaki da kungiyoyin asiri, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya tafka
- A halin yanzu 'yan sanda sun fada binciken alakar mutuwar Oloyede da basaraken, har da yasa matasa suka kore shi daga kujerarsa
Matasa a yankin Itapgbolu dake karamar hukumar Akure ta arewa dake jihar Ondo sun fatattaki basaraken yankin bayan mutuwar wani dan sanda mai suna Ayo Oloyede.
Oloyede dan sanda ne dake aiki da sashen yaki da kungiyoyin asiri dake karkashin rundunar 'yan sandan jihar Ondo kafin mutuwarsa a ranar Lahadi da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Ganau ba jiyau ba sun sanar da yadda matasa a yankin suka taru sannan suka kori basarake, Oba Idowu Faborade, Ogbolu na Itaogbolu daga fadarsa bayan labarin mutuwar Ayodele ya karade gari.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in hukumar kula da shige da fice
An tattaro cewa, marigayi Oloyede ya ziyarci mahaifiyarsa kuma yana komawa Akure ne lokacin da motar hayan da yake ciki ta kifa tare da tintsirawa tsakanin Itaogbolu da kauyen Odudu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ASP Tee Leo Ikoro, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce: "Eh mun samu bayanai wadanda ke nuna cewa wasu matasa a Itaogbolu sun tada rigima inda suka kori basarake daga kujerarsa."
"A gaskiya bamu gane alakar dake tsakanin mutuwar dan sandan a hatsari ba da kuma basaraken dake garin. Jami'anmu sun garzaya domin kwantar da tarzoman yayin da muke jiran karin bayani daga binciken." Ikoro yace.
KU KARANTA: Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5
A wani labari na daban, a kalla sojoji bakwai na rundunar sojin kasan Najeriya ne suka rasu bayan wani abu mai fashewa wanda 'yan ta'addan Boko Haram suka dasa ya fashe a jihar Borno, Premium Times ta ruwaito.
Wannan harin ya zo kasa da mako daya bayan nada sabon shugaban sojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya.
An nada Yahaya a ranar Alhamis da ta gabata bayan mutuwar tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama.
Kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, babban hafsan soja da wasu kananan sojoji hudu sun samu miyagun raunika sakamakon fashewar abun.
Asali: Legit.ng