A Wurin Gwamnatin PDP Mara Basira Muka Gaji Matsalar Ta'addanci, APC

A Wurin Gwamnatin PDP Mara Basira Muka Gaji Matsalar Ta'addanci, APC

- Jam'iyyar APC mai mulkin kasa ta ce a wurin gwamnatin PDP mara 'basira' ta gaji matsalar ta'addanci

- Jam'iyyar na APC ta yi wannan furucin ne a matsayin martani ga gwamnan RIver, Nyesome Wike da ke sukarta game da rashin tsaro

- APC ta ce idan yan Nigeria za su iya tunawa kafin ta karba mulki, yan ta'dda na kai hari kasuwanni, wuraren ibada da wurin taron mutane

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce ta gaji kallubalen tsaro da ke addabar kasar nan ne daga gwamnatin jami'yyar Peoples Democratic Party (PDP), mara 'basira', The Cable ta ruwaito.

Jam'iyyar mai mulkin kasar ta yi wannan furucin ne yayin martani kan kalaman da aka danganta da gwamna jihar Rivers Nyesome Wike, wanda ya dade yana sukar gwamnatin APC kan tabarbarewar tsaro a kasar, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A Wurin Gwamnatin PDP Mara Basira Muka Gaji Matsalar Ta'addanci, APC
A Wurin Gwamnatin PDP Mara Basira Muka Gaji Matsalar Ta'addanci, APC. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindigan da suka sace ƴan Islamiyya a Neja sun nemi a biya N110m kuɗin fansa

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, John Akpanudoedehe, sakataren kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa, ya ce kafin Buhari ya hau mulki, yan ta'adda na kai hari kasuwanni da wuraren ibada a sassan kasar amma an dakatar da hakan.

"Idan yan Nigeria za su iya tunawa yan ta'adda sukan kai hari kasuwanni, wuraren ibada da wuraren taruwar mutane a jihohin kasar nan kafin gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta karfafawa sojoji gwiwa da makamai don durkake yan ta'addan," a cewar Akpanudoedehe.

"Abin mamaki ne mai mulkin kama karya da ke gidan gwamnatin jihar Rivers ya manta cewa kamar ta'addanci, ba a gwamnatin nan ne aka fara garkuwa da mutane don neman kudin fansa ba, amma ana yin duk mai yiwuwa don magance matsalar tare da yan bindiga," in ji shi.

KU KARANTA: An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina

Ya cigaba da cewa gwamnatin APC ta kasance tana aiki a koda yaushe domin inganta Nigeria kuma ba za ta biye wa PDP da yan Nigeria suka juya wa baya a 2015 da 2019 ba.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel