Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in hukumar kula da shige da fice
- Miyagun 'yan bindiga sun sheke shugaban hukumar kula da shige da fice na Najeriya, reshen jihar Imo
- An gano cewa 'yan bindigan sun tsare shugaban a daren Asabar yayin da yake tuka motar hukumar NIS
- An samu gawarsa a daji sannan motar ta bayyana caccake da harsasai duk da basu taba komai dake tare da shi ba
'Yan bindiga sun halaka shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Imo, Okiemute Mrere.
An kashe Mrere ne daren Asabar kan babban titin Owerri zuwa Fatakwal dake Owerri, The Punch ta gano hakan a ranar Litinin.
Babban jami'in hukumar ya tabbatar da hakan inda yace an ga gawar shugaban a daji da safiyar Lahadi.
An zargi cewa Mrere na tuka wata mota kirar Hilux mallakin hukumar shige da ficen yayin da aka tsare shi sannan aka harbe shi.
KU KARANTA: Bidiyo da hotunan tsuleliyar budurwa 'yar Najeriya da ta fara tuka jirgin sama a shekaru 17
KU KARANTA: Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS
Majiyar ta sanar da cewa miyagun basu dauka bindigar da ke tare da jami'in ba saboda an ganta tare da gawarsa washegari. Sai dai kuma an ga motar hukumar da ya hau caccake da harsasai.
Majiyar tace: "'Yan bindiga sun kashe shugaban hukumar kula da shige da fice, reshen jihar Imo, Okiemute Mrere. An kashe shi a daren Asabar yayin da yake tuka mota kirar Hilux ta hukumar.
"An tsinta gawarsa washegari da safiyar Lahadi. Ba a dauka komai nasa ba, hatta bindigarsa karama. An samu motar caccake da harsasai. Hukumar ta girgiza, kowa yayi shiru saboda firgicin da ya shiga zukatan jami'an sakamakon mummunan lamarin."
Mai magana da yawun hukumar, Winifred Ogu ta ki daga dukkan kiran da aka dinga mata.
A wani labari na daban, kungiyar hadin kai tare da habaka tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ta dakatar da kasar Mali daga cikinta bayan yin juyin mulki sau biyu a kasar.
An yanke wannan hukuncin ne bayan taron gaggawa da ECOWAS tayi a kasar Ghana a ranar Lahadi, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda Shirley Botchwey, Firayim minista na kasar Ghana yace, an yi hakan ne domin tabbatar da dawowar mulkin damokaradiyya a kasar Mali.
Asali: Legit.ng