Ambasada Babagana Kingibe ya samu babban mukami a Gwamnatin Shugaba Buhari

Ambasada Babagana Kingibe ya samu babban mukami a Gwamnatin Shugaba Buhari

- Babagana Kingibe ya zama Jakada na musamman zuwa yankin tafkin Chadi

- Aikin Ambasada Kingibe shi ne kokarin kawo zaman lafiya a wannan yankin

- Kingibe ya taba rike kujerar Minista da Sakataren Gwamnatin Tarayya a baya

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ambasada Babagana Kingibe a matsayin Jagada na musamman zuwa yankin Chadi.

Gidan talabijin na TV ya fitar da rahoto cewa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya fitar da sanarwar a jiya ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, 2021.

Babagana Kingibe zai rike kujerar Jakadan musamman mai cikakken ikon mukami a fadar shugaban kasa zuwa kasar Chadi da yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: Buhari ya hadu da Shugaban rikon kwaryan kasar Chadi

Kara karanta wannan

An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

Jaridar Punch ta ce sanarwar tana cewa:

“Wannan nadin mukami a matsayin Jakada na musamman da shugaban kasa ya yi, ya zo ne bayan matakin da aka dauka a taron shugabannin kasashe da gwamnatocin yankin tafkin Chadi a game da halin da ake ciki a kasar Chadi a ranar 25 ga watan Mayu, 2021.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Jakadan musamman zai dauki nauyin wasu ayyuka da suka hada da":

"Lura da cigaban da ake samu a yankin tafkin Chadi, tare da kokarin kawo sulhu da dawo da mulkin farar hula a karshen shugabancin rikon kwaryan gwamnatin soji, sannan hada-kai da sauran kasashe da abokan hulda da nufin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali."

KU KARANTA: Buhari ya nada sabon Hafsun Sojan kasa

Ambasada Babagana Kingibe ya samu babban mukami a Gwamnatin Shugaba Buhari
Ambasada Babagana Kingibe a Aso Villa Hoto: www.dailynigerian.com

Jawabin ya cigaba da cewa, daga cikin aikin sabon Jakadan akwai:

Kara karanta wannan

Sunayen da Aka Kara da Wadanda Aka yi Watsi da su a Kwamitin Neman Takarar Tinubu

“Inganta duk wani tsari da zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Chadi, Arewa maso gabashin Najeriya da daukacin yankin tafkin Chadi.”

Ambasada Kingibe kwararren jakada ne wanda ya rike kujerar sakataren din-din-din, sakataren gwamnati, Minista, kuma ya shiga zaman sulhun Najeriya da Chadi.

Da wannan mataki, shugaban Najeriya ya nuna da gaske yake yi wajen kawo zaman lafiya kamar yadda ya yi wa shugaban Chadi, Janar Mahamat Deby Itno, alkawari.

Bayan kisan Idris Deby, idan za ku tuna shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin shugaban kasar zai haifar da babban gurbi a wajen yaki da Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel