Buhari yayi martani kan kisan Ahmed Gulak, ya bayyana matakin dauka
- Shugaban kasa Muhammadu ya bayyana damuwarsa da fushinsa kan kisan gillar da aka yi wa Ahmed Gulak
- Ya ce miyagun mutane ne da basu son hadin kai, zaman lafiya da kuma cigaban kasar nan suka yi hakan
- Buhari ya sha alwashin cewa babu wanda zai sha cikin miyagun da suka yi mummunan aikin nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa da fushinsa a kan abinda ya kira da "mummunan kisan gillan dan siyasar Adamawa Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo, wanda wasu 'yan bindiga suka yi."
A yayin martani ga aukuwar lamarin a ranar Lahadi, shugaban yace: "Na matukar fusata da kisan gillar da miyagun mutanen da basu son zaman lafiya, hadin kai da kuma cigaban kasar nan suka yi wa Gulak
"Bari in ja kunne, babu wani mutum ko kungiya da zata yi irin abun nan ta tafi ba tare da fuskantar hukunci ba. Za mu yi amfani da dukkan karfinmu wurin tabbatar da cewa wannan mummunan al'amari da miyagun mutane basu sha ba."
KU KARANTA: Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da yawon jirgin sama ranar zagayowar haihuwarta
KU KARANTA: Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a wata takarda da ya fitar yace shugaban kasan na mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, jama'a da gwamnatin jihar Adamawa tare da 'yan uwa da abokan arzikinsa na dukkan fadin kasar nan.
A wani labari na daban, 'yan bindiga wadanda ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne sun kai mugun hari hedkwatar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya dake Ubakala, karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Anambra.
Hedkwatar hukumar bata da tazara da inda 'yan sanda suke wadanda aka kaiwa hari tun farko a Ubakala kuma hakan ya kawo mutuwar jami'an 'yan sandan biyu, Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro cewa sun sakawa hukumar NIS bam inda ya tashi da ita sannan suka budewa jami'an dake aiki wuta, lamarin da ya kawo ajalin wasu daga ciki.
Daily Trust ta tabbatar da yadda wasu ababen hawa dake farfajiyar wurin aka banka musu wuta kuma suka kone kurmus.
Asali: Legit.ng