Da duminsa: ECOWAS ta dakatar da kasar Mali saboda yin juyin mulki sau 2 a wata 9

Da duminsa: ECOWAS ta dakatar da kasar Mali saboda yin juyin mulki sau 2 a wata 9

- Kungiyar ECOWAS ta dakatar da kasar Mali bayan yin juyin mulki karo na biyu a cikin wata tara

- Kungiyar ta tabbatar da cewa sai bayan Mali ta koma mulkin farar hula sannan zata koma cikinta

- ECOWAS ta yanke wannan hukuncin ne bayan taron gaggawa da tayi a kasar Ghana ranar Lahadi

Kungiyar hadin kai tare da habaka tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ta dakatar da kasar Mali daga cikinta bayan yin juyin mulki sau biyu a kasar.

An yanke wannan hukuncin ne bayan taron gaggawa da ECOWAS tayi a kasar Ghana a ranar Lahadi, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda Shirley Botchwey, Firayim minista na kasar Ghana yace, an yi hakan ne domin tabbatar da dawowar mulkin damokaradiyya a kasar Mali.

"Dakatar da kasar Mali da ECOWAS tayi zai fara aiki ne a take har zuwa watan Fabrairun 2022 lokacin da ake tsammanin zasu mika mulki ga zababben shugaban kasa," Botchwey yace.

KU KARANTA: Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS

Da duminsa: ECOWAS ta dakatar da kasar Mali saboda yin juyin mulki sau 2 a wata 9
Da duminsa: ECOWAS ta dakatar da kasar Mali saboda yin juyin mulki sau 2 a wata 9. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS

"Daya daga cikin hukuncin shugabannin kasashe shine tabbatar da cewa an saka firayim minista na farar hula wanda zai tabbatar da kafuwar sabuwar gwamnati."

Daily Telegraph ta ruwaito cewa, shugaban kasan rikon kwarya, Bah N'Daw da firayim minista Moctar Ouane a makon da ya gabata an tsaresu a sansanin sojojin kasar bayan juyin mulkin da sojin suka yi.

N'Daw, wanda shine tsohon ministan tsaron kasar Mali, an nada shi shugaban kasa na rikon kwarya a watan Satumban da ya gabata bayan sojin kasar sun kwace ragamar mulkin kasar daga hannun shugaban kasa Ibrahim Keita.

N'Daw da Assimi Goita, shugaban sojin, aka nada domin su rike kasar na wucin-gadin tsawon watanni 18 bayan nan za a yi zabe.

Shugabannin ECOWAS sun matsantawa sojin kasar akan su mika mulki ga farar hula tun bayan juyin milkin da suka yi a ranar 18 ga watan Augustan 2020.

Tuni ECOWAS ta saka wa kasar Mali matakan ladabtarwa tun bayan juyin mulkin.

A wani labari na daban, 'yan bindiga wadanda ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne sun kai mugun hari hedkwatar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya dake Ubakala, karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Anambra.

Hedkwatar hukumar bata da tazara da inda 'yan sanda suke wadanda aka kaiwa hari tun farko a Ubakala kuma hakan ya kawo mutuwar jami'an 'yan sandan biyu, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa sun sakawa hukumar NIS bam inda ya tashi da ita sannan suka budewa jami'an dake aiki wuta, lamarin da ya kawo ajalin wasu daga ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel