Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS

Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS

- Sabon shugaban sojin kasa, ya samu mukaminsa a ranar Alhamis daga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari na babban kwamandan sojojin kasar nan, shi ke da hakkin nada COAS

- Amma kafin nan, akwai wasu abubuwa da dole ne shugaban kasan ya duba kafin ya yanke hukuncin wanda zai nada

A ranar Alhamis, 27 ga watan Mayun 2021 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa na Najeriya.

Legit.ng ta tattaro wasu dalilai biyar da zasu iya zama abinda shugaban kasan ya duba kafin nada Yahaya a wannan babban matsayi.

KU KARANTA: Hotunan matashi mai shekaru 23 yayi wuf da fitacciyar 'yar siyasa mai shekaru 45

Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS
Dalili 5 da zasu iya zama abinda yasa Buhari ya nada Manjo Janar F Yahaya COAS. Hoto daga @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

1. Gagarumin sadauki ne

Manjo Janar Yahaya hafsan soja ne amma kuma sojan yaki ne. Shugaban sojin Najeriyan ya ga kusan komai a rundunar sojin kasar nan.

Kafin wannan nadin, shine mai baiwa rundunar Operation Hadin Kai umarni, masu yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Ana ware wannan matsayin ne kuwa ga hafsin sojan da yake da ilimi ayyukan soja tare da gogewa, da kuma sanin tsarin yadda aiki a filin daga yake.

2. Duban yankin da ya fito

Rundunar soji tana da manyan mukamai hudu kuma ko gwamnatin baya tana zaben shugabannin ne biyu daga kudu, biyu daga arewa.

Shugaba Buhari ya cigaba da wannan al'adar tun daga 2015. Bayan mutuwar Attahiru, an koma biyu daga kudu, daya ne dan arewa. Nadin Manjo Janar Yahaya ne ya kawo daidaituwa a tsakani.

KU KARANTA: Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki

3. Yankin da ya fito daga arewa

Bayan zaben shugabannin sojin biyu daga arewa, ana sake duba yankinsu a arewacin Najeriya. Kafin hawan Attahiru, shugabannin sojin Buhari daga yankin arewa maso gabas suke, sai kuma Attahiru wanda yazo daga arewa maso yamma hakazalika Manjo Janar Farouk Yahaya.

4. Ya kammala karatu a aji na 37 a NDA

Ana ta tsammanin shugaban kasa zai nada wani daga aji na 35, 36 ko 37 saboda manjo janar dake wadannan azuzuwan suna da kwarewa tare da gogewa kuma sune ke rike da manyan mukamai na sojin kasa.

Tabbas Yahaya ya dace, shine tsohon sakataren rundunar sojin kasa, tsohon GOC kuma ya halarci makarantar horar da hafsin soji da jami'ar Salford.

5. Jihar da ya fito

Shugaba Buhari na nada shugabannin sojinsa daga jihohin da rikici ya tsananta. Ya nada Buratai a lokacin da Borno ke fama da Boko Haram, Attahiru kuwa a lokacin da Kaduna ke fama da 'yan bindiga sai kuma Yahaya a lokacin da 'yan bindiga ke barazanar kwaceta.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya.

Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.

Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel