Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai 200 a Makarantar Islamiyya a Neja
- Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari kauyen Tegina a jihar Niger
- Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa maharan sun shiga garin a kan babura suna ta harbe-harbe
- Majiyoyi sun kuma ce yan bindigan sun hallaka mutum guda sannan sun sace 'yan Islamiyya a kalla 200
A kalla dalibai 200 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai garin Tegina a karamar hukumar Rafi na jihar Niger.
Wani mazaunin garin mai suna Zayyad Mohammed ne ya tabbatarwa Channels Television hakan a wayar tarho.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan
A cewarsa, wani tsohon jami'in hukumar kula da shige da fice ne ya gina makarantar islamiyyar mai suna Salihu Tanko Islamiyya a garin na Tegina.
Babu cikakken bayani game da harin a yanzu amma dai majiyoyi sun ce makarantar islamiyya ce irin wadanda mutane ke tura yaransu karatu ba na allo ba kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.
KU KARANTA: Bahaushen Da Ya Riƙe Amanan Bayarabe Tsawon Shekaru 30 Ya Sha Yabo
An harbe mutum daya har lahira yayin da daya na mawuyacin hali sakamakon harin da yan bindigan suka kai misalin karfe 4.30 na yammacin ranar Lahadi.
Kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Niger ba ta ce komai ba game da harin da yan bindigan ko kuma sace daliban.
A bangarensa, Sanata Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya shima ya tabbatar da harin amma bai ambaci sace yan makarantar islamiyyar ba
A cikin rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce wani mai sarautar gargagjiya ta tabbatar masa cewa yan bindiga sun afka garin na Tegina a jihar Niger.
Ya ce sun zo da muggan makamai sun sace mutane sun tafi da su cikin daji.
Ya rubuta, "Wani mai sarautar gargajiya a yankin ya sanar da ni cewa mintuna 30 da suka shude yan bindiga sun afka kauyen Tegina a jihar Niger. Sun zo kan babura da muggan makamai kuma sun sace mutane sun tafi da su daji. Mutanen garin da dama yanzu suna fitowa daga inda suka buya."
Asali: Legit.ng