Lai Mohammed Ga ’Yan Najeriya: Ku Kwantar da Hankali, Najeriya Na Cikin Aminci
- Minista Lai Mohammed ya kara wa 'yan Najeriya kwarin gwiwa game da halin da ake ciki
- Ya bayyana cewa, Najeriya na cikin aminci duk da halin matsalar tsaro da ake fuskanta
- A cewarsa, ya kamata 'yan Najeriya su guje wa duk wani mummunan hasashe da ake wa kasar
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar na cikin aminci a hannun shugaba Buhari duk da kalubalen tsaro da ta ke fuskanta, The Punch ta ruwaito.
Ya shawarci ‘yan kasa da kada su yarda da mummunan hasashe game da Najeriya saboda ba za su zo ba.
Ministan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye da mukarrabansa a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.
KU KARANTA: Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga
“Idan ana magana game da tsaro, ina so in yi amfani da wannan dama in tabbatar wa 'yan Najeriya cewa duk da kalubalen tsaro da muke fuskanta a yanzu, Najeriya na cikin aminci. Dole ne mu ki amincewa munanan hasashe game da kasarmu saboda ba za su cika ba.
"Yana da mahimmanci ga shugabanninmu a kowane mataki su bai wa mutane kwarin gwiwa maimakon yin kalamai da ka iya kara kawo tashin hankali," an nakalto Ministan yana fadi a cikin wata sanarwa a shafin na ma'aikatar.
KU KARANTA: Ministan Buhari: Idan Talakawa Suka Nemi Na Tsaya Takarar Shugabancin 2023, Zan Yi
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin jirigin ruwa a jihar Kebbi, lamarin da ya bayyana a matsayin mummuna.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a matsayin mummunan lamari, a cikin wata sanarwa ta hannun babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, The Nation ta ruwaito.
Shugaban ya yabawa wadanda ke ci gaba da aikin ceto tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan murmurewa cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng