An tashi: Chelsea ta doke Man City 1-0 a wasan karshe a gasar Zakarun Turai

An tashi: Chelsea ta doke Man City 1-0 a wasan karshe a gasar Zakarun Turai

Kungiyar Kwallon Chelsea da Man City na karawa a wasar karshen na gasar gwanayen Turai.

Legit Hausa na kawo muku bayanai kai tsaye kan yadda wasan ke gudana a kasar Fotugal

KAI TSAYE: Chelsea 1-0 Man City (Wasan kwallon karshe a gasar gwanayen Turai)
KAI TSAYE: Chelsea 1-0 Man City (Wasan kwallon karshe a gasar gwanayen Turai)
Asali: Twitter

An tashi, Chelsea ta zama Zakarun Turai na Bana

An tashi: Chelsea ta doke Man City 1-0 a wasan karshe a gasar Zakarun Turai

Bayan cikan mintuna 90, An kara minti 7

Alkalan wasa sun kara mintuna 7 bayan cikar mintu 90 na farko a wasar karshe na gasar Zakarun Turai na 2021

An cire Raheem Sterling, Aguero ya shiga

Bayan taka leda na kimanin mintuna 74, An cire Raheem Sterling, Aguero ya shiga

Rudiger ya jiwa Kevin De Bruyne rauni, an yi waje da shi

Kyaftin na Man City, De Bryne ya yi kicibis da mai tsaron bayan kungiyar Chelsea kuma ya samu rauni sakamakon haka, an maye shi da Fernandinho.

Chelsea ta zura kwallo daya

Dan wasan Chelsea Kai Havertz ya yanke mai tsaorn gidan Man City kuma ya zura kwallo guda yayinda ake gab da zuwa hutun rabin lokaci

Online view pixel