Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Ƙasar Musulunci Ba, In Ji Jikan Shagari

Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Ƙasar Musulunci Ba, In Ji Jikan Shagari

- Bello, jikan tsohon shugaban kasar Nigeria, Shehu Shagari ya ce Nigeria ba za ta taba zama kasar musulunci ba

- Bello ya kuma ce bai taba goyon bayan shari'a a Nigeria ba yana mai cewa ba dai-dai ake yin shari'a a kasar ba

- Sai duk duk da hakan, ya ce yana kare shari'a domin akwai wadanda ba su fahimce ta ba suke tsangwamarta

Bello Shagari, jikan tsoho shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya ce Nigeria ba za ta taba zama kasar musulunci ba.

Tsohon shugaban na kasa na kungiyar matasan Nigeria, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, ya kuma ce irin shari'ar da ke yi a Nigeria ba bisa ka'ida ake yi ba.

KU KARANTA: An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Kasar Musulunci Ba, Inji Jikan Shagari
Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Kasar Musulunci Ba, Inji Jikan Shagari. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya rubuta, "Da farko, ban taba goyon bayan shari'a a Nigeria ba. Ana iya gani kararara cewa Nigeria ba kasa bace ta shari'a kuma ba za ta zama kasar shari'a ba.

"Sai dai, na kasance mai kare shari'a saboda masu tsangwamar musulunci a Nigeria a maimakon aiki da shi yadda ya dace.

KU KARANTA: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

"Kada kowanne mai addini ya tursasa addininsa a kan wasu, ko Allah ya yi umurni da cewa 'babu tilas a addini'. Don haka, tilastawa wasu musulunci ba koyarwar addinin musulunci bane.

"Bayan shari'a, babu wata doka da ake yin ta dai-dai a Nigeria. Don haka, a lokacin da muke sukar shari'a, muyi taka tsan-tsan kada mu kushe ta baki daya, domin shar'a a kansa umurni ne a musulunci, don haka sukarsa ci fuska ne ga musulmi da tsangwamar musulunci."

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel