Gwanda mu daina yaudarar kanmu, abubuwa sun tabarbare a kasar nan: Sarkin Musulmi

Gwanda mu daina yaudarar kanmu, abubuwa sun tabarbare a kasar nan: Sarkin Musulmi

- Sultan Na Sokoto ya halarci taron tattauna matsalar tsaro da Najeriya da fama da ita

- Sarkin gargajiyan ya yi kira ga shugaban kasa ya sauya dabaran yaki

- Jiharsa na Sokoto na cikin jihohin da yan bindiga suka addaba a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, a ranar Laraba, ya ce yan Najeriya su daina yaudarar kansu cewa abubuwa na tafiya daidai a Najeriya.

Sultan Saad ya bayyana hakan ne a taron tattauna matsalar tsaro dake gudana a Abuja, rahoton Channels.

"Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwa na tafiya daidai, abubuwa sun tabarbare. Mun san hakan, kuma muna gani," Sultan yace.

"Abubuwa sun yi muni yanzu. Ba ka bukatar wani ya fada maka Najeriya na cikin halin ha'ula'i kuma wannan shine gaskiya."

Sarkin ya yi bayanin cewa a shekaru 11 da yayi matsayin Sarkin gargajiya, ya halarci tarukan tattauna matsalar tsaro a Najeriya da dama, kuma lokaci ya yi da shugabannin zasu tashi tsaye maimakon surutai.

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

Gwanda mu daina yaudarar kanmu, abubuwa sun tabarbare a kasar nan: Sarkin Musulmi
Gwanda mu daina yaudarar kanmu, abubuwa sun tabarbare a kasar nan: Sarkin Musulmi Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Sultan ya yabawa Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila, kan shirya wannan taro.

Ya yi kira gareshi ya tabbatar da cewa an aiwatar da shawarin da aka samu bayan taron.

Sarkin ya bayyana farin cikinsa cewa Kakakin majalisar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad, sun amince abubuwa sun lalace a kasar nan.

Najeriya na fama da matsalolin tsaro ta kowace fuska.

Daga Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, zuwa matsalar yan bindiga a yankin Arewa maso yamma, sai kuma rikicin manoma da makiyaya a Arewa maso yamma, yan ta'addan IPOB a kudu maso gabas da kuma garkuwa da mutane a Kudu maso yamma.

A bangare guda, Mai alfarma Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar III da Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye sun yi kira ga gwamnati ta sake dabara wajen yakar matsalar rashin tsaro.

Da suke magana jiya, manyan sarakunan sun bayyana cewa ba zai yiwu gwamnatin tarayya ta cigaba da amfani da dabara daya, ta na tunanin ta ga sauyi ba.

Jaridar The Nation ta ce Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a rage surutu, a dage da aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng