Mutum 5 Sun Mutu Yayin Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai Ofishin Ƴan Sanda a Delta

Mutum 5 Sun Mutu Yayin Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai Ofishin Ƴan Sanda a Delta

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ofishin yan sanda a Umutu jihar Delta

- Yan sandan da ke caji ofis din sun yi musayar wuta da yan bindigan inda aka rasa rayuka biyar

- Yan sanda biyu sun mutu yayin gumurzun yayin da daya ya mutu a asibiti sakamakon hawan jini, a bangaren yan bindigan biyu suka mutu

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari caji ofis na yan sanda a Umutu a karamar hukumar Ukwuani a jihar Delta hakan ya yi sanadin mutuwar mutane biyar.

Vanguard ta ruwaito cewa wadanda suka mutun sun hada da jami'an yan sanda uku da biyu daga cikin yan bindigan sakamakon musayar wuta da suka yi yayin harin.

Mutum 5 Sun Mutu Yayin Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai Ofishin Ƴan Sanda a Delta
Mutum 5 Sun Mutu Yayin Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kai Ofishin Ƴan Sanda a Delta. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Ragargaji 'Yan IPOB, Sun Kashe 7 Sun Kama Biyar a Rivers

Da ya ke tabbatar da harin, mai magana da yawun yan sandan jihar Delta, Mr Bright Edafe cikin wata sanarwa ya ce, "Asafiyar yau 28 da watan Mayun 2021 a misalin karfe 1.30, yan bindiga da dama sun afka ofishin yan sanda na Umutu.

"Sun bude wuta sai dai saboda tsaurara matakan tsaro da kwamishinan Delta ya saka aka yi, yan sandan da ke caji ofis din sun mayar musu da wuta.

"Yan bindigan sun juya a yayin da suka lura ba za su iya cin galaba kan yan sandan ba. An kashe biyu cikin yan bindigan yayin gumurzun, an kuma raunata wasu.

"Sun dauke gawar yan uwansu sun tsere. Rundunar yan sandan ta rasa jami'ai biyu yayin da wani ASP ya rasu sakamakon hawan jini a asibiti.

KU KARANTA: Buhari Ya Sabunta Naɗin Garba Abari a Matsayin Shugaban NOA

"Yan bindigan da suka zo da niyyar kona ofishin yan sandan ba su yi nasara ba domin sun gaza shigowa caji ofis din, ba a rasa makamai ba kuma ba a kona caji ofis din ba, lamura sun koma dai-dai yadda suke.

"Kwamishinan yan sanda ya bawa mutane tabbacin cewa rundunar za ta kama wadanda ke wannan harin tana mai kira ga mutane su rika taimaka mata da bayanai masu amfani."

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel