Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS

Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS

- Tsananin farin ciki da annashuwa ta bayyana a cikin sojojin Najeriya bayan nadin sabon shugaban sojin kasa

- A ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu ne aka tattara sojojin inda aka sanar dasu labarin nadin sabon COAS

- An nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa bayan mutuwar Laftanal Janar Ibrahim Attahiru

Lokacin farin ciki ne da annashuwa ga sojojin Najeriya dake gaban daga yayin da aka sanar dasu cewa Manjo Janar Farouk Yahaya aka nada a matsayin shugaban sojin kasan Najeriya.

A wani bidiyo da wani @Abbakar1030 ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, ya nuna yadda sojojin ke ihu cike da murna bayan an sanar dasu labarin.

KU KARANTA: Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki

Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS
Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS. Hoto daga @Abbakar1030
Asali: Twitter

Zakakuran sojin sun nuna jin dadinsu bayan da aka sanar dasu labarin mai faranta rai. Ga bidiyon yadda murnar ta kasance:

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 6 da ya dace a sani game da Manjo Janar F Yahaya, sabon COAS

Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban sojin kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya. Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.

Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya. Kamar yadda hedkwatar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon darakta janar na hukumar yaki tare da hana safarar mutane (NAPTIP).

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.

Shehu yace shugaban kasan ya amince da wasu manyan sauye-sauye a ma'aikatar tallafi da jin kai tare da walwalar 'yan kasa.

Shehu yace an dauka wannan matakin ne domin a samar da burin gwamnati na tabbatar da aiki mai kyau a cikin hukumomin biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel