Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai, ya kai Naira Tiriliyan 32 a mulkin Shugaba Buhari

Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai, ya kai Naira Tiriliyan 32 a mulkin Shugaba Buhari

- Najeriya ta karbo aron kudin da ya haura Naira Tiriliyan 20 a shekara biyar

- Daga tsakiyar 2015 zuwa 2020, DMO ta ce bashin Najeriya ya karu da 170%

- A halin yanzu bashin da ake bin gwamnatin kasar ya zarce Naira Tiriliyan 32

Daga watan Yulin 2015 zuwa karshen shekarar Disamban 2020, adadin bashin da ke kan wuyan gwamnatin Najeriya ya tashi da Naira tiriliyan 20.8.

Jaridar Punch ta ce alkaluman da ta samu daga ofishin tattara bashi na kasa, DMO, ya nuna haka.

Gwamnatin tarayya ce ta ci duk mafi yawan bashin nan da ake magana. Sama da 80% na bashin da ake bin kasar ya na kan wuyan gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Bashin da ake bin Najeriya ya kara yawa

Daga cikin wannan adadi na Naira tiriliyan 32.92, gwamnatin tarayya ce ta karbo kusan Naira tiriliyan 27, yayin da aka bar jihohi da Naira tiriliyan 6.

Bayanan da aka samu daga DMO sun kara nuna cewa an karbo fiye da 62% na wannan bashi ne a cikin gida, Naira tiriliyan 12.71 ne aka karbo daga ketare.

A daidai tsawon wannan lokaci, shekara biyar da rabi, gwamnatin Najeriya ta kashe sama da Naira tiriliyan 10 wajen biyan tsofaffin bashin da ta ci a baya.

An biya bankunan gida Naira biliyan 485 daga watan Yunin 2015 zuwa karshen wannan shekarar.

KU KARANTA: Ko karin 1% aka yi a kan kudin fetur, za mu tafi yajin aiki - NLC

Bashin da ake bin Najeriya ya tashi sosai, ya kai Naira Tiriliyan 32 a mulkin Shugaba Buhari
Zainab Ahmed Shamsuna Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Idan aka yi lissafi a kudin Naira, daga Yunin 2015 zuwa Disamban shekarar 2020, gwamnatin Najeriya ta maida Naira tiriliyan 8.53 da ta aro a cikin gida.

A cewar DMO, daga cikin wadannan makukun kudi, abin da Najeriya ta aro daga kasar Sin ya kai Dala biliyan 3.7. Jaridar Tribune ta fitar da wannan rahoton.

Idan za ku iya tuna wa, a lokacin da Muhammadu Buhari ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2015, bashin da ake bin kasar bai wuce Naira tiriliyan 12.1 ba.

Amma zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2020, bashin ya tashi zuwa Naira tiriliyan 32.92. Hakan ya na nufin an samu karin 171.62% cikin watannin 66 da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel